An kafa wannan ƙungiyar a shekara ta 1986.

Ayyukan tallafi a Nijar

A karshen shekarun 1980, AECIN kadai ce tushen kudade RAEDD, ta samu damar kaddamar da farko shirinta na “Kowane ɗan makaranta na da littafi na kowane fanni”.

Tallafin da AECIN yake kawo wa RAEDD ya ɗauki fannoni daban-daban kamar

  • Binciken samun wasu abokan tarayya
  • Rubuta buƙatun samun kudade
  • Sa ido kan ayyukan Nijar da rubuta rahotanni
  • Har ya zuwa 2011, tattaunawa tare da matasa Faransawa masu sha’awar zuwa Nijar don ayyana waɗanda aka horar da su
  • Tarbon membobin RAEDD a Faransa
  • Rubuce-rubuce Ƙasidu ranar 13 ga watan Mayu, ranar matan Nijar, daga shekara 2005 zuwa 2014 tare da RAEDD
  • Rubuce-rubuce da wallafawa tun daga shekarar 2015 ta Mujallar Tarbiya Tatali wacce ake bugawa sau biyu a shekara
  • Kirkira da sanya idanu kan shafin yanar gizo ta Tarbiyya-Tatali
  • Nisha (shakatawa) a Faransa.

Inganta al’adun Nijar

AECIN ta shirya nune-nunen abubuwa da yawa, musamman gamme da hotunan Alain Roux, an buga littattafai guda huɗu, waɗanda ƙungiyoyi Faransawa da na Nijar suka haɗu don gyarasu da wallafasu. A Makarantar gatannan Nijar, Nijar, a wani lokaci can baya da Lugu da Sarauniya da Tarihin Kwanawa, kazalika da littafin Shaidun tsofin ɗalibain makarantar mai gemu a Dogondutsi (Nijar). An yi bugawa ta biyu na Lugu da Sarauniya da Tarihin Kwanawa, tare da hadin gwiwa gidan buga littatafai mai suna Harmattan.

ku shiga AECIN ! ku goyi bayan ƙungiyar AECIN !

Adareshi :

AECIN Tarbiyya Tatali

c/o Michel Coste

6 A Mail de Bourgchevreuil

35510 Cesson-sévigné
Talho : 02 99 83 30 98
Yanar gizo : aecin@tarbiyya-tatali.org

 

Articles liés

Archives