Shawara ga masu tafiya.

Kafin ka fara tunanin tafiya zuwa Nijar, Leka wurin ba da shawara kan tafiye-tafiye wanda ake bayanawa dangane da yanayin tsaro.

Akwai wuraren yawon buɗe-ido ko’ina cikin yankunan ƙasar Nijar.

Tun daga wuraren
shaƙatawa masu ƙayatarwa, zuwa abubuwan gargaziya masu kyau.
Sai dai kaɗan ne daga cikin su aka inganta.

Jahar Yamai

Bayan gidan kallo da keɓaɓɓun wuraren ayyukan hannu na gargajiya, da hada-hadar manya da ƙananan kasuwanni, da abubuwan da cibiyar al’adu na hulɗar ƙasar Faransa da Nijar ‘’CCFN’’ take gudanar, akwai yawo cikin kwalo-kwalo da ake iya yi bisa babban gulbin ‘’Isa’’ don ziyartar manyan kasuwanni kamar kasuwar Ayoru, ko Balleyara, ko kuma zuwa kure don ganin raƙumman daji da suke yawo cikin daji tare da samun kariya daga al’umman yankin.

Yankin nammun daji ‘’Parc W’’

Yankin ne mai ƙayatarwa da yake bakin iyakokin ƙasar Nijar da Benin da Burkina Faso. Ya ƙunshi giwaye, da zakuna, da barewu, da birwai da ɗimbin zabbin daji da ake iya saye, a dahe ko a gashe, lokacin abincin dare.

Jahar Agadas

Jaha ce wanda ƴan yawon buɗe-ido suka fi sani saboda manyan duwatsun Ayir (‘’Aïr’’), da kwarangwal na wasu halittun can da, da ake tonowa daga cikin ƙasa, da kuma kyakkyawun tudunnan rairan hamada.

Kayan aikin hannu iri-iri

Akwai kayan aikin hannun da ake yi kamar sarƙa da ƴan kunne, da abubuwan fata, da na saƙa, da na aikin laka.

Girafe de Koure