Kiwon lafiya yana cikin mawuyacin hali

Fiye da mutum guda cikin biyu, ba su samun amfanin gidajen likita. Likitoci da kayan aiki sun yi kaɗan. A cikin shekarar 2014, likitoci 5 ke akwai don mazauna 100,000. Wannan ƙididdiga tana ƙasa ga rabin ta gayiyayun ƙasashe na duniya.
Kuma magani ya yi tsada sosai. Fiye da 45% na yawan jama’a suna rayuwarsu da layin talauci a cikin shekarar 2014.

Lafiyar uwa da ta yaro

Yawan mace-macen mata masu juna biyu kuma, 509 ne ke mutuwa wajen haihuwa bisa 100,000 (a shekarar 2017) har yau
yawan mace-macen jarirai 80 ake samu cikin 1,000 (a shekarar 2018). A cikin shekarar 2016, 31% na yara ba su da nauyin da ya kamata su yi, kenan yunwa ta kama su.

Bambanci ga yankuna

Al’ummar birni ta fi ta karkara samun zuwa likita, ko da yake kashi 84 cikin 100 na mutane a ƙauye suke rayuwa.

Ƙaramcin kasafin kuɗi

Rabo na kasafin kudin kiwon lafiya a kasafin kudin kasar ya kai kashi 7.2% a shekarar 2015, yayin da ƙungiyar lafiya ta duniya wato OMS ta bayar da shawarar kashi 10% ne ya dace.

Gwamnati ya girka wani tsari na kokowa da talauci, cikinsa akwai sashen kiwon lafiya. Aikinsa ragagge ne saboda ƙarancin kuɗi.

Tsafi