Karatun boko

Cikin babban birnin ƙasar, da wasu manyan birane, yawancin yara suna yin karatun boko. Amma cikin ƙauyuka, yara da yawa ba su zuwa makarantar boko, kuma yawan ƴan mata bai kai ba ga na ƴan maza. Faransanci shi ne harshen koyarwa, yara ba su amfani da shi gidajensu, sai dai wata sa’a.
Yara da yawa da suka je makarantun boko ba su ida firamare. Cikin ƴan makaranta 100, waɗanda ba su samu suna da yawa. Babban ƙoƙarin da aka yi ga ci-gaban makarantun firamare ya sa a shekara ta 2008 an samu kashi 60 cikin 100 na yara da suka je makaranta duka faɗin Nijar. (ƴan mata kashi 53 cikin 100 sun je makaranta).

Kayan aiki cikin makarantu

Ba su isa ba sosai : ba issasun malamai, ba issasun makarantu, ba issasun littattafai. Ƴan makaranta sun yi yawa cikin azuzuwa. Wasu malaman suna da aji biyu masu yaro hamsin (50) cikin aji. Don haka aka yi wannan tsarin : aji guda da safe, aji guda da marece.

Tilas ne a yi tunani a samo hanyoyin horo a makarantun da suke ba iyayen yara wani nauyi kuma a riƙa horon malamai ko suna cikin ayyukansu. Ƙasar Nijar ta fitar da wani tsari na shekara 10 (goma) na ci-gaban makarantu mai yin kira ga duk al’umma kuma da taimako daga ƙungiyoyi masu zaman kansu, Akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu kamar ‘’Aide et action’’ da take gina azuzuwa ko kuma tana tai da mutanen gari su samu malamai na gida don su ɗauki wirin da malamai suka tafiyarsu.

Ci-gaban ayyukan makarantu za su sa a samu dubban ƴan makarantar kwaleji, ko da yake ba a shirya kome ba na maraba da su : makarantu da tsarin ilimi.

Cikin wannan halin ne muke tafiyar da ayyukan horo a makaranta.

Fête à Lougou le 13 mai 2007