Duk wani aikin ci-gaban al’umma, ba ya da inganci sai wanda yake kyautata rayuwar al’ummar, kuma ya zamanto al’ummar ce take tafiyar da ayyukan ci-gabanta.

Ga tsarin ayyukanmu

 • Bisa bukatun jama’a
 • Tattarawa da tsara kayan aiki
 • Neman Ƙokarin kowa
 • Bin al’adun al’umma
 • Aiki tare da hukumomin yankin
 • Kowane aiki yana da nashi tsari da keɓabbun Kuɗin yin shi
 • Sarrafa ci gaban ayyukan da kuma amfani da kudade

Kurakuran da ya kama ta kauce wa

 • Rashin dacewa da buƙatu
 • Rashin dacewa da al’adu
 • Aikin da ya a amfana da shi gobe
 • Rashawa da almubazzaranci

Fusa’o’inmu na aiki

 • Mutanen da al’umma ta amince da su ne ake zaɓa
 • Harshen mutanen garin ne ake yin amfani da shi
 • Ana kafa dandalin hira.
 • Akwai lokaci na yin nazari
 • Ana yin aiki da matakan da al’umma ta ɗauka
 • Rubutaccen rahoto akan tsari da na kuɗi na kowane aiki
 • Sarrafawar ziyaru
 • Ana yin gwaji, san nan a tabbata, kuma a yaɗa