Kididdigar Ci Gaban ‘yan Adam (IDH) wani ɗan gajeren labari ne wanda ƙungiyar Ci gaban ƙasashen ɗinkin Duniya ta ƙirƙiro don auna ci gaban ɗan adam na kowace ƙasa. Yana la’akari da tsaran rayuwa daga haihuwa, matakin ilimi gami da kayan cikin gida na kowane ɗan Adam.
Nijar tana cikin jerin kasashen da ke da mafi karancin tsarin ci gaban dan Adam (daga ita sai na ƙarshe). A cikin shekarar 2018 Ana iya bayyana wannan musamman ta hanyar tsayon rayuwa, yanayin rayuwa da matakin ilimi da suka ragu sosai a ƙasar. Tabbas, ɗan Nijar ba shi da damar rayuwa sama da shekara 60 kuma ba zai yi makaranta sama da shekaru 5 ba. Matsayi ne mafi ƙarancin ilimi a duniya. Bugu da kari, matsakaicin ɗan Nijar yana rayuwarshi da kasa da $ 1,000 a shekara.

Amma dai, ya kamata a cancanta ƙaramcin darajar ƙasar. Nijar tana da arziki da yawa, musamman ta albarkatun ƙasa (uranium, mai, gas, zinariya). Sai dai, wani lokacin ba a ganin arzikinta ta hanyar karuwar saboda yawan jama’a (kashi 3.8 a kowace shekara akan matsakaita). Ana iya bayanin wannan musamman ta hanyar yawan haihuwa a duniya saboda Nijar ce ta ɗaya, a adaɗin haifuwa, kamar yara 6 ga kowace mace a matsakaita a shekarar 2017, da kuma karuwar shekarun rayuwa tun haihuwa.
Bisa ga wannan a ƙara wahalar samun tabbatattun bayanai a cikin ƙasar da ke fuskantar da babban canji har yanzu.

Amma idan muka lura da canjin ci gaban ɗan Adam a Nijar, muna iya ganin an samu ci gaban, tunda IDH ya tashi daga 0.21 a shekarar 1990 zuwa 0.38 a shekarar 2018. Idan aka yi la’akari da adaɗin tun daga sherarun 1990, ana iya cewa tsawon rayuwa ya karu daga shekaru 49 zuwa shekaru 56. Har yanzu a ƙasan jeri, Nijar na ci gaba duk da cewa matakin ilimi ya kasance diddigen da ta kasa shawo wa kai.

Wannan labarin ya dogara ne akan rubutun da Eliot Martin ya yi game da aikinsa tare da AESCD a watan Satumba na 2020.

Karin bayani: https://www.populationdata.net/pays/niger/