
À la Une


Ilimi ta hanyar wasanni motsa jiki

Cikin harshen hausa, Tabiyya Tatali na nufin ‘’Taimako kan ci-gaban kai da kai’’.
Babban maƙasudin wannan rukinin ƙungiyoyi a fannin makarantu na Nijar da na Faransa shi ne taimaka wa ƙoƙarin da al’ummar Nijar ta ɗauki nauyin tafiyar da ci-gabanta mai ƙarko, tare da yin kira ga taimakon ƴan ƙasa kuma da taimako daga ƙasashen duniya da kuma ba da kuzari ga sanar wa juna al’adun gargajiya.
Tarbiyya Talali ta ƙunshi : A Nijar, ƙungiyar RAEDD (Rukunin ƙungiyoyi ne mai kula da ci-gaba mai ƙarko wajen ayyukan makarantu) ; A Faransa, ƙungiyar AECIN (ƙungiya ce mai sanar wa juna al’adun gargajiyar tsakanin Ille da Vilaine Niger), da ƙungiyar AESCD (ƙungiya ce ta taimakon juna tsakanin garin Cesson (a ƙasar Faransa) da garin Ɗankassari (a ƙasar Nijar)), da ƙungiyar ANIRE (’ƴan Nijar ta Rennes). A ƙasashen Faransa da Nijar, duka waɗannan ƙungiyoyin suna neman abokan hulɗa kuma suna tattara kuɗin taimako. Suna sa hannu ga rayuwar ƙungiyoyi a ƙasashen Faransa da Nijar.
A Nijar | A Faransa | |
Ƙungiyar RAEDD | Ƙungiyoyi na rukunin ƙungiyoyin Tarbiyya Tatali. | |
Tana nazari bisa halin da karkara take ciki. | Suna sa a san ƙasar Nijar, | |
Tana yin huroje dabam-dabam, | Suna shirya taruwa da kula da abubuwan da suke faruwa, | |
Tana yin ayyuka wuri ɗaya. | Suna bi sau da ƙafa ayyukan da ake yi a Nijar. |