A Nijar, har yanzumata suna fuskantar bambanci da wariya wajen zartar da dokoki da al’ammurran rayuwa. A cikin matsalolin da matan suke fama da su akwai auren latse da na dole, da rashin cikakkar lafiya tabbatatta, da rashin samun horo isasshe da wuraren noma, da rashin adalci wajen rabon sakamakon noma, da kuma rashin dokokin zaman iyali. Akwai kuma rashin sanin dokoki ga mazan da matan.
A cikin abubuwan da Tarbiyya Tatali ta sanya a sahun gaba cikin tsaretsarenta, akwai kyautata rayuwar mata da irin jan ƙoƙarinsu ga ayyukan ci-gaba a fannoni kamar na hororwa, da na kiwon lafiya, da na yaƙi da talauci, da na inganta al’adu.

Shigarmu cikin ƙungiyar CONGAFEN

Tarbiyya Tatali, mamba ce ta haɗin gwiwar ƙungiyoyin mata na Nijar cewa da CONGAFEN wadda aka haƙiƙanta zamanta tun 1995. Gurin farko da CONGAFEN ta sanya gaba shi ne ta ba sauran ƙungiyoyin farar hula damar haɗa kansu don gudanar da ayyukan kyautata jin daɗin rayuwar matan Nijar.

 

Articles liés

Archives