Carte du Niger

Mahimman Abubuwa

 • Faɗi ƙasa : muraba’in kilomita 1 267 000 (murabi’in kilomita miliyan da dubi ɗari biyu da sittin da bakwai)
 • Yawancin al’umma suna zaune guduncin ƙasar.
 • Ƙasar tana nesa da bakin teku.
 • Babu hanyar jirgin ƙasa.
 • Hanyoyin motaci ba su da kyau wanibi.
 • Akwai babban kogin kwara a yammacin ƙasar.
 • Hannuwan kogi biyu sun ƙeƙashe : su ne tsohon kogin Boso da tsohon kogin Mawri, a kudu.
 • Akwai babban dogon dutsi mai suna Aïrn, a arewacin ƙasar.
 • Babban sashen ƙasar Hamada ce a Arewa.

Manyan sassa

 • Sashen Aïr : yankin Cirozerin inda birnin Agadas yake.
 • Sashen Manga : Yankin Difa
 • Sashen Zarmaganda : Yankin Doso
 • Sashen Gobir : Yankin Maraɗi
 • Sashen Adar : Yankin Tawa
 • Sashen Zarmaganda : Yankin Tilaberi
 • Sashen Damagaram : Yankin Zandar
 • Babbar birnin Yamai.