Yunwar da aka yi a shekara ta 2005, ta nuna rishin ingancin noma a ƙasar Nijar. Al’umma tana ƙaruwa, wuraren noma suna sallacewa, ruwan sama suna ƙaranci, kuma fara tana yin ɓanna sosai. Bayan haka, sassan hukumomi ba su da dataccen tsarin shawo kan matsalla idan ta abku. In kuma ba a yi hantali ba, za a ci gaba da fuskantar matsaloli har shekaru na gaba saboda dole ne talakawa su rungumi basussuka don rayuwarsu. Idan suka sayar da cimakar da suka samu domin biyan basussukan, babu shakka za su komawa gurbin jiya na ƙarancin abinci tun ƙarshen lokacin damana.

A shekara ta 2012, wata yunwa mai tsanani ta sake abkuwa a ƙasar Nijar.

Bugu da kari, daga 2015 ambaliya ta hallaka dukan amfanin gona na wasu iyalai.

 

Articles liés

Archives