A Nijar muke aiko kuɗin abubuwan da muke sayarwa; bayan wannan, abubuwan suna ba da damar sanin ƙasar Nijar, da al’ummarta, da irin yanayinta, da kuma al’adunta.

Lugu da Sarauniya

Tarbiyya Tatali da gidan wallafawa littattafai mai sunan Harmattan suka yi wallafawa ta biyu na littafin tare da yi masa yan gyare-gyare. Ana sayda littafin “Lugu da Sarauniya” euros 19. Ana iya aika shi ta gidan waya. Command. Ana amfani da illahirin kuɗaɗen da aka samu na littattafai, don bunkasa ci gaban ayyuka na al’ummar Lugu.

Tarihin Kwanawa

Tarbiyya Tatali da L’Harmattan suka wallafa wannan littafi na Dangaladima Issa Danni Soumana, mai kumshe da al’adun baka, da gabatar da tarihin kwamin ɗin Kwanawa da suke a jihar Dogondutsi, a Ƙasar Nijar.

Littafin dai kuɗinsa euros 19 ne.
Kuna iya sayen shi, a aka maku shi.

Makarantar gidan mai geme wato mission ta Dogon Dutsi

Sakamokon aikin da Antoine Leocur ya yi a shekarar 2008 lokacin da ya je zaman cuɗayyar juna tare da Tarbiyya Tatali, wannan ɗan littafin yana ƙumshe da taƙaitattun shaidu na tsofin ɗaliban makarantar gidan masu gemu wato mission ta Dogon Dutsi.
A na iya sayen littafin, kuɗinsa euros 5. Ana iya aika shi, ana iya odar shi : oda

Littafin gatanai mai sunan ‘’Gatan gatanku : an yi wani lokaci a Nijar...’’

Ana sayar da wannan littafin a yuro 5 (wajen jika 10 kenan). Idan ta hanyar saƙon wasiƙu ne, to zai tashi a yuro 18, tunda yuron 3 na bisa su ne na aiko saƙon. Duka kuɗin da ake samu ga littafin, a Nijar ake aiko su don aiwatar da ayyukan ci-gabon ƙasar.

Littafinmu na farko na gatanai mai suna ‘’Gatanan ƙasar Nijar’’, ya ƙare.

Katocin gatanai

A albarkacin fitowar littafin ‘’Il était une fois au Niger’’, an buga katocin goma sha biyar (15) dabam dabam na zagayowar shekara. Kowace kati ta ƙunshi hoton da Abdul Aziz Sumaïla ya aka ɗauka a wurrin mai gatana, kande ko Isa, tare da zuban ɗaya daga cikin gatanan. Kuɗin yuro 1 (dala 135) ake sayar da kati guda. Tarin duka gatanan ya tashi yuro 15.
A game da waccan littafin gatanan ‘’A l’école des contes nigériens’’, katoci 9 aka yi daban daban masu ɗauke da hotunan da Alain Roux ya yi, a kuɗin yuro 1 kowace kati.

Katocin gaisuwa ko hotunan kahe.

Akwai katoci masu hotunan launin baƙi da fari na Alain Roux bisa’’ Enfants du Niger’’ wato ’ƴaran Nijar’’; yuro 4 ake sayar da hotuna 9 (a ƙayyade girman katin ko na hoton kahen)
Akwai hotuna masu launi na Alain Roux bisa ‘’Rayuwar yau da kullum a Nijar’’ ‘’Vu quotidienne au Niger’’ yuro 4 ake sayar da hotuna 10 (a ƙayyade girman katin ko na hoton kahen).

Raka mu da gudummuwar kuɗi

Kuna iya raka mu ko kuma ku aiko ma AECIN ko AESCDgudummuwar kuɗi, kuna iya faɗin aikin da kuka kawo ma goyon baya.

Adireshi

Ana iya aiko kowane irin saƙo, ko takardar ‘’shak’’ na banki’’, ko odar wani abu a wannan adireshin :

Tarbiyya Tatali AECIN

C/O Marie – Françoise Roy

6A Mail de Bourgchevreuil

35510 Cesson – Sévigné

Idan odar wani abu ne, ku aika a layin ‘’intanat’’ : aecin@tarbiyya-tatali.org.