Lugu

Garin Lugu yana cikin Dapartaman Dogon Dutsi a cikin ƙasar Nijar, mai nisan kilometir 350 da Birnin Yamai. Gari ne mai cikakkun al’adu da mahimmin tarihi. Nan ne cibiyar al’adun azna ; matsafa ne, kuma nan ne mazamnin Sarauniya wadda ikonta yake ci yau da ƙarnoni da yawa.

Sarauniya

Wata sarauniya ce mai suna Ƴar kasa da ta zo daga Daura a arewacin Nijeriya, bayan wani rikici da ya haɗa ta da ƴan uwanta. Dutsin da ake ce ma Tunguma ne ya yi mata jagora har ya kawo ta yankin da ake kira Arewa yanzu, ko kuma ƙasar mauri, inda ta kafa garin Lugu. Sarauniyoyin Lugu sun riƙe iko da shugabancin addinin ƙasar mauri (Arewa) har lokacin zuwan ‘’Vule’’ da ‘’shanuwan’’ turawa ƴan mulkin mallaka a shekara ta 1899, inda suka tarwatsa garin, bayan wani gagarumin faɗa wanda ya sa Sarauniya Mangu gudun hijira.

Tammahar sake rayuwar Lugu

A can da, rukunin garuwa ne masu arziki ; amma a halin yanzu, Lugu ya talauce, kuma al’umma ta rage. Kamar ga al’ada, Sarauniya Aljimma tana rayuwata a gefe guda cikin bukkarta ; babu wani sauran mulki, amma an san shugabancinta a fannin addini a cikin yankin, har ma a ƙetare.
Tun shekara ta 2001 ne akafara ganin hasken rayuwa a Lugu, tare da ayyukan ci-gaban yankin da ake zartarwa, ta hanyar ƙungiyoyin farar hula da na mata. Lugu da Sarauniya sun fara maido sunansu.

A shekarar 2013, an kafa wurin samun tsabtatun ruwan zamani, wannan ya sa garin ya hwalhwado, taimakon ya zo daga gwomnatin Nijar da kuma rarraba hadin gwiwa tsakanin yankunan karkarar Dankatsari da Lugu da commun din Cesson-Sévigné ta Bretagne.

“Lugu da Sarauniya”, wallafawa ta biyu

An wallafa littafin tare da taimakon Tarbiyya Tatali da gidan wallafawa mai sunan Harmattan.

Nicole Mulin, Bube Namaiwa, Marie-Françoise Roy da Bori Zamo, mambobin Tarbiyya Tatali na Faransa da na Nijar,suka rubuta littafin da aka sayda a Faransa da Nijar. An yi amfani da kuɗaɗen da aka sayda Littattafai na wurin Tarbiyya Tatali don bunkasa ci gaban ayyuka na al’ummar Lugu, musamman a fannin ilimi.