Mahamadou Saidou, octobre 2015 (Photo d’Abdoul Aziz Soumaïla)

An haifi Mahamadu Saidu wajen shekarar 1952 a Dogon Dutsi, Nijar, a matsayin wani ɓangare na babban iyalin Kwanawa. Su 19 ne, amma ba dukansu suke uwa ɗaya uba ɗaya ba, saboda mahaifinsa ya auri wasu mata. Bayan makarantar firamare a makarantar mai gemai (Mission) ta Dogon Dutsi, karantun sakandare ya kai shi zuwa samun jarabawar ƙarshen karatun sakandare wato bac D. Daga nan kuma ya tafi ya yi nazari a jami’ar kimiyya ta Yamai amma bai samu damar kammalawa ba sai ya zama malami kwaleji.

Ya tuntuɓi IREM (Institut de Recherche sur l’Enseignement des Mathématiques) ta Yamai, idan ya zama malamin nazari da shire-shiren ayyukan IREM a Zinder a shekarar 1982.

Mahamadu ya koma karatu a jami’a ta zama malaman kwaleji (Faculé de Pédagogie), sai ya zama farfesa na kwaleji a Yamai. Yana aiki sosai a IREM har ma yana zuwa a Faransa don ƙara samun horo a matsayin wani ɓangare na IREM na Rennes (akwai kuɗaden mu’amala). Ranar 22 ga watan decemba mahaifinsa ya rasu, sai ya zama shugaban gida, kuma ya koma Dogon Dutsi don sake tsara iyalin. Wannan ya sa ya ɗauki nauyin biyan kuɗaɗe makaranta na ‘yan uwansa maza da mata.
An kwana biyu da suka yi aure tare da Philomene wadda ita ce kawai matarsa, ba su da ’ya’ya amma sun ɗauki riƙon yara dayawa kamar dai yadda ake a ƙasashen Afirka.

Da ya dawo a Yamai, ya halarci taron Conférence Nationale Souveraine wadda ta kawo mulkin demokraɗiyya. Yana cikin ɓangaren ƙungiyoyin masu kullawa da jama’a, a matsayin shugaban ƙungiyar Wasannin Ilmin Lissafi ta Nijar. A lokacin ne ya fara siyasa a PNDS wato Party na Nijar mai kullawa da demokraɗiyya, da gurguzanci. (Parti Nigérien pour la Démocratie et le Socialisme).
Mahamadu ya so ya karfafa karatunsa amma bai samu dacewa ba. Wani tsohon darektan IREM na Rennes da ya zama darektan IUFM (Cibiyar Jami’a ta Horon mallamai) ya ce zai iya ɗaukar bakuncin shi. Kuma wasu abokansa na Faransa suka kula da sauran: tiketa na jirgin sama, da kuɗaɗen zamansa a Faransa. A Nijar, kuma yana a matsayi horo wannan ya ba shi damar ci gaba da kullawa da iyalinsa, har kuma da samun damar ajiyar ƙudi. A lokacin nan ne ya gina gidansa a Tallague.

Ya yi karatu na shekaru uku (1993 zuwa 1996) da suka ba shi damar samun Diploma na Lasisi, Master da DESS a bagaren kimiya ta horo wato Sciences de l’Education, a Jami’ar Rennes 2. A wannan lokacin ne kuma ya kafa ƙungiyar Tarbiyya Tatali, tare da sa hannun aminan dayawa da ya yi duk inda ya zamna. Ƙungiyoyi a Nijar da Faransa, suna aiki tare, domin ci gaban da jama’ar Nijar. Aikinsu ya dogara ne a kan girmama juna, abuta da kuma musayar al’adu.

Mahamadu ya koma Nijar inda ya zama mashawarcin INDRAP (Institut National de Documentation, de Recherche et d’Animation Pédagogiques), har sai da ya yi ritaya, yana da shekaru 55 da haifuwa. A wannan lokacin ne ya kafa RAEDD (Réseau d’Actions Educatives pour un Développement Durable), wanda shi ne shugaban tsare tsaren ayyuka har ranar rasuwarsa a 2016. A Faransa, François Hébert ya kafa AECIN (Association d’Echanges Culturels Ille et Vilaine Niger) wanda Yvon Logeat, Marie-Françoise Roy, Tifenn Leclercq Michel Coste da Alice Belliot a yau, suka zama shugabanin ta.

Shirin farko na Tarbiyya Tatali, na sayan littattafai na firamare don hayar su, ya kai kimanin CFA 350 000 (kimanin kudin Euro 500) cikin kuɗin AECIN. RAEDD kuma tana ta ci gaba tare da gudummuyar ƙungiyoyin tarayya dayawa (ofisoshin, manyan ƙungiyoyi masu zaman kansu, ...) kasafin kuɗinta na shekara ya kai euros 250 000.

Mahamadu kuma mai faɗi a ji ne a PNDS musamman ma a cikin ƙungiyar yakin neman zaben shugaba. Samun ikon shugaban ƙasa na Issoufou Mahamadou a shekarar 2011, ya sa Mahamadu ya zama matsayin dirakta na ofishin Ministan Ilimi da bunƙasa harshunan gida.

Abin ban sha’awa ya yi aiki a fani uku : aikin sarushi ko aikin mulki, , siyasa da aikin cikin ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Amma wannan haɗin ayyuka (dirakta na ofishin Ministan Ilimi da bunƙasa harshunan gida, shugaban ƙungiyar RAEDD, siyasa) ya gajiyar da shi sosai . A watan Nuwamba shekarar 2015, ya halarci jana’izar Sarkin Arewa a nan ya faɗi, yana fama da cutar bugun jini. An riƙe shi likita, kuma ya koma gida, sa’an nan kuma aka kai shi Morocco sau biyu, kuma aka kara komawa da shi asibiti... A ra’ayin Sieyaba ’yar’uwarsa, “Ba mai iya cewa an gano asalin cutar shi .”
Ya mutu a babban asibitin Yamai ran 6 ga watan Agusta 2016.

Tun lokacin, zuwa yanzu Tarbiyya Tatali tana ta samun ta’aziyya, masu bayyana bakin ciki da asarar da aka samu. Mutane da yawa suna ta yabon Mahamadu Saidu bisa kunzarishi, fara’arsa, hakurinsa, da kuma ikon sauraren mutane da Alla ya ba shi . A Faransa kamar a Nijar membobin Tarbiyya Tatali sun ɗauki alƙawalin ci gaba da ayyukan mutumin nan wanda ba kamarsa.

Mahamadou Saidou, coordinateur de Tarbiyya Tatali au Niger (1952-2016)