Tarbiyya Tatali tana nufin “Taimako wajen samun ci gaban” a cikin harshen Hausa.

Manufar wannan kungiyar ta ‘yan Nijar da ta ‘yan Faransa ita ce don ta tallafawa jama’ar Nijar wajen tsunduma a cikin tsari na raya kasa; Tattara karfi na kasa da kuma na kasa da kasa da kuma inganta musanyar al’adu.

Mu’amala da ci gaba

Yadda za a yi yaƙi da jahilci, gina mulkin demokraɗiyya, yaƙi game da cin hanci da rashawa, kafa tattalin arziki, tabbatar da’yancin kan kasa, tare da nazarin abubuwan da wasu kasashe suka yi, don kiyaye wasu lamurai da kuskure. Taimakon abukai a kan wasu matsaloli na Nijar na da muhummanci wajen ilimantar da halin da ake ciki da kuma samun mafita.

 

Dans cette rubrique