Hulɗa shiri ne na aikace aikace da gunduma biyu suke yi, ɗaya a Faransa (kwomin, hukuma, jiha, yanki) guda kuma cikin wata ƙasa. Wannan tsari dai da yardar gundumomin nan biyu ake yin shi. Duka biyun suna kawo taimakon su. Wannan tsari na sa a samu taimokon kudi dayawa wajen wadansu abokan hul’da. Kungiyoyin dayawa, da ma masu zaman kan su suke tallafawa wajen ci gaban wannan tsarin. (A Faransa da kuma a cikin ‘kasar guda)

A yi sa hannun hul’da tsakanin birnin Cesson-Sevigne da gundumar Dankatsari a shekarar 2009. Ba’a yanka mata ‘kayyade ba. Kungiyoyin AESCD A Faransa da RAEDD a Nijer suke da nauyin ‘bunkasar ta ita. Daga shekarar 2013, an samu sabon mataki game da aikin ci gaba na dukan kauyukan Dankatsari, wanda ya hada da abokan tarayya da dama. An kammala wannan aikin a farkon 2017. Wani sabon tsari "Ci gaba wajen mamufofi bunkasa rayuwa (ODD) a garuruwan Dankatsari" ci gaban ayyukan rani na shekara ta 2017.

An sa hannu akan sabuwar yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Cesson-Sévigné da yankunan karkarar Dankatsari, na tsawon shekara 2018-2020, tare da yarjejeniya tsakanin birnin Cesson-Sévigné da AESCD.
An sake sabunta yarjejeniyar a 2021-2023.

Za a sadaukar da kuɗin birnin Cesson-Sevigne wajen :

  • iikace-aikace na inganta ’yancin mata da kiwon lafiyarsu,
  • ci gaban tattalin arziki da samun ƙananan rance don inganta ayyuka masu kawo kudi,
  • wurin horo.

Har ila yau, waɗannan kwomin biyu na tafiya hannu cikin hannu wajen haɗin gwiwa don inganta dukan ayyukan ci gaba na Dankatsari, ta hanyar amsa kiran gayyata daga jama’a ko hukumomi.

Hadin gwiwar Cesson-Dankassari da dukkan abokan kawancen ta sun sa baki a fannoni da dama na zamantakewar al’umma kuma ta aiwatar da ayyuka da yawa tun shekarar 2009, a zaman wani bangare na ci gaban dukkan kauyukan Dankatsari, wanda ya hada abokan hulda da yawa.

Duba na 2009-2013, na 2013-2016, na 2017-2018, na 2018-2020 da na 2021-2023.

 

Ayyuka masu daidaituwa don ci gaba mai ɗorewa na ƙauyukan Dankatsari

Rahoton kan haɗin gwiwar Cesson-Sévigne da Dankatsari 2009-2021

Articles liés

Archives