Yanayi mai daɗi, da maras daɗi sun sha bamban a ƙasar Faransa da ta Nijar.

A ƙasar Faransa idan samaniya ta ɗauki launin bula, kuma ba a yin ruwa, shi ne yanayi mai daɗi.

A ƙasar Nijar, lokacin da ake yin ruwa, shi ne yanayi mai daɗi.

Kasancewar shekara a Nijar

Watan Afirili da farkon watan Mayu, lokaci ne na tsananin zafi inda cutar sankarau da cutar dussa suke yin ɓanna sosai ga jarirai da yara ƙanana.Lokaci ne inda yunwa ta fara kunno kai, tunda tanadin cimakar shekarar baya ya ƙare, kuma ana shirye-shiryen damana mai zuma.

Ruwan sama suna farawa a cikin watan Mayu

Idan aka samu makarar damana, ko kuma ruwan ba su isa sosai ba, to damuwa ta samu a game da yadda sakamakon noman za ya kasancewa, da yadda za a ƙetare lokacin rani.
Amma da zaran ruwan sama sun sabka sosai, farin ciki ne ga kowa; sai aikin gona tuƙuru kodayake cirmakar bara da aka yi tanadi ta yi kusan ƙarewa. Dukan guraben ruwa na ƙasar suna sake cikewa, ga kuma tsanwa ko’ina.

A cikin watan oktoba ne ake ɗibar (fidda) cimaka

Hatsi shi ne cimakar da aka fi amfani da ita.

Daga watan Nobamba zuwa Feburairu, lokacin nan ne na yanayi mai daɗi a Faransa.

Lokaci ne inda samaniya take daukar launin bula, rana tana fitowa, kuma ana yin sanyi da dare. Akwai lokuttan da iska mai Tsakuwa da ƙura yake busawa, tare da hatsarin haddasa ciwon maƙoshi.
A Nijar, daga ɗari ya yi ƙamari, to ya zama ƙorahi ko’ina ; har ma abin yakan bai wa Faransawa dariya, kodayake ba kowa yake da bargo ko rigar ɗari ba.

Daga watan Maris ne zafi yake farawa

San nan sai zafin ya ci gaba da yin ƙamari. Cimakar da aka tanada take ƙarewa. Sai jiran ruwan sama, yanayi mai daɗi, tare da shakkun samun isassun ruwa.

.

Matrones dans une case de santé