Cuɗayyar al’adu, ƙaruwar kowa ce

Kowa yana iya ganin haka a cikin rayuwarsa. A misali a ɗauki Bafaranshe da ƊAN Niger suna yin aiki iri ɗaya, kuma a wuri ɗaya, ko kuma nuna wa juna irin dahe-dahe, da sauran su.

Akwai abubuwa da yawa da mutanen Faransa suke iya kowo wajen mutanen Nijar

A bar ganin Nijar kamar tana ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci ; ƙasa ce mai bada shawa saboda tarihinta, da haɗin kai, da cuɗayyar al’ummarta, da zumunci a cikin birane da karkara ; nan da nan ake karɓar baƙo ba tare da nuna mashi kome ba. Har harshen faransanci ma mutane suna jin daɗin maganta shi da sauraren shi.

Al’ummar Nijar ta koyi abubuwa da yawa daga Faransa

Da ƙasashe masu ƙarfin arziki, kamar yaƙi da jahilcii, da yaƙi da cin hanci, da shimfiɗa demokaraɗiya, da tattalin arziki, da tabbatar da ƴancin kai, tare da gane kurakuren da ya kyautu a kauce ma. Ra’ayoyin abokai faransawa bisa wasu matsalolin ƙasar Nijar, su ma suna iya taimakawa wajen warware su.

Al’adu, wani ginshiƙin ci-gaba ne

Bai kamata a raba sanin da ake samu makarantar boko da al’adun gargajiya ba ; sai dai su tafi tare. Hankalin da faransawa suke maidawa wajen sanin al’adun gida, yana ba ƴan Nijar damar su ƙara gano al’adunsu kuma su yi murnar haka.

Photo d’Alain Roux

 

Articles liés

Archives