Al’adun galgajiya na Arewa. Jihar tana da tarihi et al’adu na asali.

Gurinmu

Bayan mummunar saduwa ta jama’ar Nijar da turawa ‘ƴan mulkin mallaka na farko, maras imani da darajja, yau gurinmu shi ne yin aiki don a samu sabuwar hanyar ta ha’din gwiwa da girmama juna da kuma sulhu tare da ha’din kan jama’a duka.

Garin Lugu, tushen Arewa

An yi tarurruka da yawa a garin Lugu, da Bagaji da kuma Dogon Dutsi don tabbatar da cewa dukan sassan yankin Arewa sun amince da Lugu ne tushen Arewa. Duka suna son a bayyana tarihin domin tsaga hanyoyin ci-gaba bisa matakan ƙwarai, ko da yake an samu faɗuwar hannu da halayen cin amana a wasu lokutta.

Kenan, da amincewar Sarauniya Aljimma ne, da kuma tattaunawa tare da mutanen garin da na yankin, muka bayyana labaru kan Lugu bisa yanar gizonmu, muka wallafa ƴan littattafai biyu a shekara ta 2005 da 2006. Haka aka buga littafin “Lugu da Sarauniya,”, sannan Tarbiyya Tatali ta sake buga shi tare da Harmatta.

Ayyukan da muka yi, da waɗanda muke hasashe

Tarbiyya Tatali ta wallafa littafai biyu na gatannai, , da wani littafi mai sunan ‘’Lugu da Sarauniya’’ da kuma wani ɗan littafi bisa makarantar gidan mai geme wato « mission » kuma muna hasashen yin wani na tarihi da al’adun Arewa don amfanin ƙananan makarantun boko, da kuma kafa wani wuri na kayan al’adun Arewa a Dogon Dutsi.
A shekarar 2015, za a buga littafin tarihin Kwanawa game da taimakon Tarbiyya Tatali da gidan buga littattafai da ake kira Harmattan. Muna da burin shirin wani littafi akan Bagagi da Baura.