Bayan wani rikici da ’yan uwanta, dutsin Tunguma ya sa, Sarauniya Yar Kasa, wadda ta zo daga Daura a arewacin Najeriya a yau, ta zama sarauniya. Ta yi zamanta a wata kasar da ba kowa, wacce yanzu ake kira Arewa ko kasar arawa, ta kafa ƙauyensu, Lugu. Ba a san ba ko yaushe aka yi abun ba, an dai san da cewa ya kasance a cikin ƙarni na 16 ko 17.

Matsayin Tunguma

Tunguma dai an san ta a duk ƙasar Nijar da sauran ƙasashe, galibi ana kiranta da Dutse na Adalci kuma ana neman ra’ayinta, saboda haka ake kiran ta da dutsen dabo, amma da alama kotunan hukuma sun rage neman ra’ayinta a fagen adalci.
Ba a ɗauki Tunguma a matsayin dutse ba amma a matsayin mai hazaka kuma mallakar Sarauniyar Lugu ce. Tunguma tana da alaƙa da iccen kuka, saboda a ƙarƙashin
iccen kuka aka fara ganinta, kuma aka ajiye ta a ƙarƙashin wani iccen kuka. Wannan iccen gidan aljamai ne kuma alama ce ta nuna samun ’ya’ya dayawa, kamar na yawan yayanta, ko’ina cikin Yammacin Afirka. A yau babu sauran bishiyar kuka da za ta tanada Tunguma. Duk bishiyoyin kuka, waɗanda suke da yawa a yankin, sun bushe saboda fari. A yau ƙarƙashin wani ɗan icce Tunguma take, wannan ɗan iccen a madadin iccen kuka na asali.

Ibadar Tunguma

Wannan sakin layi yana bayanin ladaban da muka samu a garin Lugu tsakanin 1983 da 2010.
Dutsen na kamar a kilomita uku zuwa hudu daga Lugu, a kan tuddu zuwa gabas. Yan tunguma, wadanda ke zuwa yin shawara da ita, har ma da makiyaya, mafarauta, masu son labari, suna jiran wajajen dutse isowar wadanda suka fito daga Lugu.
Maitunguma, mai kula da bikin, shi ke, zubda ruwa sau uku a kan Tunguma, yana karanta kalmomin al’ada, yayin da masu sauraro ke musayar gaisuwa tare da neman wurin zama.
“Tunguma, dutsin Daura na Katsina na Bornu, a zo da dariya, a koma da hushi” wanda ke nufin: "Tunguma, dutsen Daura, na Katsina da Bornu a zo da dariya, a koma rai a ɓace [saboda an gano mai laifi]. Mai kula da aikin ya kan aje
gorar shi kusa da dutsen. Ya buɗe raga a kusa da dutsen, sannan ya daga dutsen sau uku kafin ya aje shi, sau uku a cikin raga sannan ya bar shi wurin. Sa’anan masu ɗaukar shi biyu, da ake kira dawakan dutse ke zuwa. Maza ne ‘yan garin Lugu, diya maza (’ya’yan maza), zuriyar ƙauyen na gefen maza. Suke ɗawainiya da ita.

Kamar mai kula da bikin, masu ɗaukar ta na sanye da fararen kaya, sun cire takalmansu. Dutse yana cikin ragar mallake a sanda. Dukan suke daukewa. Suna daidaita dutsen a hankali, koyaushe wajen hanya ɗaya ake ɗaukar, yana fuskantar gabas. Ana kiranta Wannan fuskar hanci. Bayan ɗagawa da ajewar dutsen sau uku, sai su ɗauke shi a kafaɗunsu.
A lokacin wani ya kawo tulin kasa a gaban mai kula da bikin, kimanin mita takwas daga dutsen, masu kallo da sauraro suna tsaye a bayansa. Sa’a nan ya balbaje kasar. Maitunguma ya fara gaisuwa: “Ina gaisuwa Tunguma, ina gaisuwa: Ina gaishe ku Tunguma, na gaishe ku” sau uku, yayin da mai hidimar ke yayyafa wa kansa kasar da ke gabansa sau huɗu. Dutse na jan masu ɗauken shi baya. Dole ne dutse ya amsa gaisuwa, ma’ana, karba su, ya dawo sau uku a gaban mai kulla da bikin. A yi ta gaishe gaishe a daidai lokacin kuma ana ta jefa kasa, har sai Tunguma ta ci gaba. A lokacin Maitunguma sau uku ya ce: “Na gani kuma na gode”. Sannan sau uku: “Diya mazan mu na Lugu, kwana lahiya, tashi lahiya”: “Diya matan mu na Lugu, kwana lahiya, tashi lahiya, kuma sau hudu:” Diya matan mu na Lugu , kwana lahiya, tashi lahiya“: ’Ya’yan matan Lugu sun kwana lafiya, sun tashi cikin koshin lafiya.”

“Ina masu magana? ..... ku ba da goro (’yan goro ya’yan itace masu daci ne, watarana kuma kuɗi), a ajiye musu. Mai magana ya aje kuɗin. Ya fallasa matsalar shi ga mai kula da dutsin, shi kuma ya ci gaba,”To [To], Tunguma, wannan abu (kuma ya fayyace matsalar) lamarin Allah ne?“, sau uku. Idan Tunguma ta ce eh, ya kamata a yi jira, wato, babu wani abin da za a yi, wanda ba safai ba. In ba haka ba sai a duba:”Shin akwai wani abu?" - Ee. Sannan a tambaya shin hannun mutum ne ya haifar da matsalar, ko kuma aljani... da dai sauransu. A yi ta yi sai ana kawarwa, sannan a yi kokarin neman magani. Tunguma ya amsa da eh ta hanyar yin gaba har sau uku,ko yana amsawa a’a kawai. A kowace tambaya, mai hidimar yana jefa yashin kasa zuwa Tunguma. Ya sanya maganarsa a cikin yashi sannan ya share ta da ɗaukar yashin kasa.

Tsarin rufewa koyaushe za’a maimaita shi sau huɗu ga mace kuma sau uku ga namiji: “ƙasar Saraunya, kwana lahiya, tashi lahiya: ƙasar Sarauniya, yi barcin kirki, da farkawa mai kyau. Kasar Magaji, kwana lahiya, tashi lahiya: ƙasar Magaji, yi barcin kirki da farkawa mai kyau". Bayan gaisuwa iri-iri na yanayi iri ɗaya, sai a kammala: “Dokin gabanku, yi kyakkyawan barci, da farkawa mai kyau. Dokinku na baya, yi kyakkyawan barci, da farkawa mai kyau, ”ga masu ɗauka.

A shekarar 1984, bisa aiki biyu na Tunguma, tambayoyin sun ta’allaka ne akan mutuwar dabba ba gaira ba dalili, asarar wani abu, zabin wurin da za’a kafa bukka, Haihuwa tun lokacin bai kai ba, wanda dutsen ya nuna zaɓin mai warkar da matsalar, mantawa da alƙawari ga mai magani, wanda aka tsara roko (buƙata, addu’a) wurin Sarauniya, saboda rashin sadaukarwa ga mai magani. Ana kuma tambaya “Idan ba a yi wa gonar magani ba?” Da kuma: ciwo, cututtuka, rashin labaran dangi, tsoran yara.
A shekara 2005 mata biyu kishiyoyi suka zo yin shawara wurin dutsen, ɗayan tana zargin ɗayan da hana ta samun haifuwa wato idan ta samu ciki sai ya fadu kafin ya kai haihuwa. Wadda ake tuhumar ta yi kira da karfi ga Tunguma da ta wanke ta.
Tunguma a zahiri ta yi tsalle zuwa gaba, da tura waɗanda suka zo don sauraren hukuncin, don tabbatar da rashin laifin wanda ake tuhuma.
Tunguma ta sauraron dukkan tambayoyi. Sauraron shawarwarinta ba ya da tsari kamar na a zo a gani, yana da tsauri. Kowa na iya yin magana yadda ya ga dama. Mai kula da aikin wanda kamar koyaushe yana tare da ninki biyu, yana iya, idan ya gaji ko ya kasa samun tambayoyin da suka dace, mika masa hannu. Amma a wannan yanayin kuma, duk wanda ya hallari taron na iya ba da dalilan da ke iya faruwa, zuwa tambayoyin da za a yi don warware matsalar. Wasu mutane wani lokacin sukan yi tambayar da kansu tare da watsa kasa da hannuwansu. Wannan yana yiwuwa musamman ga mutanen garin Lugu. Wasu kuma suna kokarin yi wa Tunguma rada. Amma a rishin samu amsa sai a shaida masu da su yi magana da babbar murya!

Tunguma ba za a iya samu ba

A farkon shekarar 2017, X, wanda ke a ’yan kilomita daga Lugu, ya yi alfaharin lalata Tunguma da sandar ƙarfe. An watsa hotunan tarkace na abun. An kama X kuma ana tuhumarsa da “lalata kayan al’adu da addini”. Bayan watanni shida na kamu da aka yi masa, an sake X a kan beli, a watan Oktoba 2020 kafin a yanke hukuncin. Ya yarda da abun da ya yi, kuma ya nuna cewa bincike bincike da yawancin hukunce-hukuncen karya da rashawa da tunguma ta yi suka sa shi aikata hakan.

Azna Lugu da Bagaji, sun ce hotunan tarkace ba na Tunguma da aka ce an fasa ba ne. Tunguma ruhu ne wanda yake cikin dutsen kawai yayin da ake shawarwari, ba za a iya tarwatsa shi ba saboda dutsen da ya ke amfani da shi ya fashe. A gare su, Tunguma ba ta nan saboda ta tafi neman ruhohin duwatsu bakwai na Daura. Karin tabbaci a wajensu na tafiyar Tunguma, mutuwar Makera, da ke jagoranci aikin tuntuba tunguma.

An ce Tunguma ta gwammace ta tafi don kin yarda da rashin kulawar da ake shirin yi mata saboda Sarauniya ta tsufa sosai, Baura da Magagi ma haka, wasu za su yi amfani da dutsen yadda suke so, ba tare da girmama ruhun ibadar ba.

A ra’ayin waɗansu kuma, Tunguma ba ta zama dole ba tunda Nijar ƙa’idar doka ce take amfani da ita tare da shari’a na zamani.
Tunguma ba ita kaɗai ba ce a wannan halin, amma ana cewa ita ce ta ƙarshen Duwatsu Bakwai na Daura da take ci gaba da yin irin wannan aiki. Ala kulli halin, an daina yin al’adar, shafi ya juya.

Ana cewa a Lugu da Bagaji da Tunguma ba za a iya samu ba.