Lugu ta na cikin gundumar Dankasari. Gari ne wanda ya ƙumshi tarihin Arewa a cikin Nijar. Nan ne mazamnar sarauniya kuma shugabar addinin Azna.

Lugu gari ne mai fama da talauci, amma da amincewar Sarauniya Aljimma, Tarbiyya Tatali ta fara gudanar da ayyukanta tun shekara ta 2002.

Alamun farfaɗowar garin

Garin Lugu, gari ne wanda ya daɗe ba a kulawa da shi.Amma yanzu gwamnati ta fara maido hankali wajen shi. Ya fara cika da al’umma.

Matan Arewa sun yi wani taro a garin Lugu na ranar sallar mata ta 13 ga watan mayu na 2005, kuma sun ƙara yin wani a ranar 13 ga watan mayu na 2007.

An kafa a shekarar 2013 wani wurin samun ruwa na shaton ruwa, da na kankare wato, wurin ‘daukar ruwa mai pampo biyu, da pampo biyu da aka kafa, ‘daya cikin makarantar, ‘daya kuma cikin gidan lafiya.

Fim Ruwa falala Lugu yana nuna canji da samun ruwa ya kawo a cikin rayuwar garin. Lugu Daraktocin fim din wato Idi Nuhu da Saradji Bakabe ne suka wallafa shi a garin Lugu da Dankatsari.

 

Articles liés

Archives