An sanya wannan rukunin yanar gizon akan layi a ƙarshen watan Agusta 2020. Yana ƙarƙashin alhakin shugabannin ƙungiyoyin membobin Tarbiyya Tatali huɗu.

Dukkanin membobin sun kasance masu taimako ne don Allah, ba don a ba su albasi ba.
Wadda ta ƙirƙira shafin Tarbiyya Tatali Elise Coste ce tun shekarar 2004. Amaury Adon ne ya yi wannan sigar ta yanzu.
Bayyana abubuwan edita na shafin tun shekarar 2004 Marie-Françoise Roy da Mahamadu Saïdu suka yi shi, sannan Marie-Françoise Roy da Seiyaba Elhadj Saïdu, a kan takardun aikin Tarbiyya Tatali (rahotanni na wata-wata, rahoton ayyukan. ..). Rubutun labaran da sanya su a yanar gizo, Marie-Françoise ce ke yin su har zuwa Oktoba 2020. Yanzu tare da Chantal Blum, suke wannan aikin.

Fassarar labaran kuma Armelle Le Bozec ke yi a Turanci, Saude Ali Bida na yi da Hausa.

Hotunan da ke shafin na Alain Rux, Abdul Aziz Sumaïla, Jean-Pierre Esturnet, Idi Nuhu da Maman Siradji Bakabe ne ko kuma na membobin Tarbiyya Tatali daban-daban.