Tarkama dai lokacin biki ne da gawar marigayiya Sarauniya ta Lugu ke nada wadda za ta gaje ta. Sarauniya Aljimma, wadda Tarkamar Sarauniya Gado ta nada a shekarar 1983, ta rasu ne a ranar 7 ga Janairu, 2023 bayan ta shafe shekaru kusan arba’in tana mulki.

An shirya Tarkama ta Sarauniya Aljimma cikin gaggawa a ranar Litinin 9 ga watan Janairu. Bikin na bukatar halartar ƴan yankin ƙauyukan Lugu da yawa. Ana shirya gawar marigayiya a cikin babbar bukkata, wadda za a rugujewa inda an gama. Tarkama za ta zabi wurin da zai kasance a yi wa sabuwar Sarauniyar bukkat
Akan lulluɓe jikin a cikin tabarmar da aka ajiye a kan wani dandali mutane guda huɗu ke ɗaukar gawar, ɗaya a kowane kusurwa. Daga Darei ne Mazaje hudu suke, Darei wani kauye ne a cikin karamar hukumar Dankatsari da Bagagi, wani kauye a cikin gundumar Matankari. Mutumin da yake rike da gatari kuma yana buga kasa idan ya tambayi Tarkama ya fito ne daga Guilme, a cikin yankin Dogonkiria, yana tare da wata mata wadda kan buga wata kwarya da aka kifar da ita a kan wata mai dauke da ruwa, da kuma wani mawaki mai ganga.
A waje, taron jama’a sun hallara, mata da ’yan mata daga nesa suke kallo, maza da samari suke matsowa. Jami’ai na zaune a kan kujerun kamar su Kona Dogondutsi, Hakimin Sashen, Hakiman Dankatsari da Dogondutsi, Wakilan Sarkin Arewa da na Hakimin Tibiri da kuma ‘yan kungiyar RAEDD. Gendarma na nan don tabbatar da a yi sabgar lafiya. Limaman Azna suna zaune a kasa, ana iya gane su game da kayan ado da farar hularsu. Sama da mata goma ne aka tara, wadanda suka cika sharuddan zabe su, kuma mazaunan kusa da Lugu.
Da zarar an kammala shirye-shiryen, Tarkama ke fitowa daga babbar bukka. Yanzu dai ana yin bikin ne a bainar jama’a. Sai ta fara zuwa dajin da ke kewayen ƙauyen, aikinta shi ne ta samo wata allura da aka ɓoye a wurin. Wannan matakin yana tabbatar da cewa Tarkama ta cika aikinta. Idan ta komo cikin ƙauyen sai ta gaida hakimai sannan ta gaida limaman Azna.
Mutumin da ke da gatari ya bugi kasa ya ambaci sunayen matan da suka taru daya bayan daya. Idan Tarkama ta zabi daya, dole ne ta bayyana ta ta hanyar zuwa saman kanta. Haka aka zabi Aljimma a shekarar 1983, abin ya ba ta mamaki. Amma a wannan karon ba ta zabi ko ɗaya daga cikin waɗannan matan ba.
Bayan sun gaisa da limaman Azna, sai Tarkama ta tafi ƙauye neman gidan sarauniyar da za ta kasance a nan gaba. Da zarar an samu gidan, sai a tambaye ta ta fadi matar gidan da ta zaba, wacce za ta yi sarauta a nan gaba. Ta zabi Kambari wacce aka haifa a Lugu, tana zaune a Tudun-Barewa, inda mijinta da ya rasu ya zauna. Ba ta nan a Lugu. An shaida wa ’ya’yanta saboda dole ne su yi bankwana da ita, ba za su kara samun damar ganinta ba. Aka dauke ta a mota, zuwa Lugu kuma yanzu tana zaune a can (duba karin bayanin labarin Sarauniya Kambari a karshen Mujalla).
Lugu ta sami sabuwar sarauniya, Sarauniya Kambari.
Tarkama ta gama aikinta. Mawaka da matasa, suka tona kabarin Aljimma, a wurin da Tarkama ta gano. Za a binne gawarta da fatar sa. Yanzu za ta huta a Lugu a makabartar Sarauniyoyi.
Aziz Sumaïla wanda Tarbiyya Tatali ta aika zuwa Lugu da zarar aka ce mana yana iya halatar taron ya dauki hoto da video na Tarkama don yin rubutu akan bikin. Culture Plus tare da haɗin gwiwar AECIN suka shirya wani ɗan gajeren fim. A saninmu, wannan shi ne karo na farko da ake yin fim ɗin Tarkama a birnin Lugu. Godiya ta musamman ga al’ummar Lugu bisa irin tarbar da suka yi da kuma hukumomin karamar hukumar Dankatsari bisa goyon bayansu.