Shaidun tsofin ɗaliban makarantar « mission » ta masu gemu

Wannan ɗan littafin dai yana ƙumshe da sakamakon binciken na Antoine Lécour. Abu ne mai daraja masamman wajen sani Nijar da kuma yadda wasu manya ma’aikatanta suka samu horo. Binkicen dai yana ƙumshe da tattaunawa da ya samu tare da tsofin ɗalibai 10 na makarantar gidan mai geme wato « mission » ta Dogon Dutsi. Antoine ya fara wannan aiki a shekarar 2008, amma Dominique Berlioz da

Makarantar gidan mai geme wato « mission » a da

A shekara 1941 Mai gemu Constant Quillard, ɗan mishan ya iso Dogon Dutsi. « Ina cikin jin daɗi, game da kwancin hankali. Wani abu ya ce mini a nan zan fara aikina kuma a nan zan kafa bukkata ta farin » Makarantar gidan mai gemu dai su suka ƙera ta a shekarar 1947, kuma har yau, makaranta ce mai jin kanta duk cikin Nijar saboda tana cikin ɗaya daga makarantun da suka hora manya ma’aikatan ƙasar. Saɓani da makarantun gwamnati wadanda da sai yaran masu gari ko kuma yaran yan garin kusa da makarantu, makarantar mai gemu dai a daji take zuwa neman yara gari ko na kewaye, babu dai banbanci ko kaɗan. Ba dan wannan ba, da dai a cikin su ba wanda ya je makaranta. Makarantar mai gemu wato « mission » ita ce ta sa kuma suka dace. To yawancin su dai yau malaman makaranta ne, wasu kuma ƴan jarida ne, ko ƴan aikin mulki, ko kuma ƙananan parepe, ko malaman makarantar jami’a.

Dukansu dai na dage game da sa’ar da ƙaddarar da ta sa suka je wannan makarantar. Ganin ƙwafin yara da damuwar uwaye, ya sa masu gemu tare da goyon bayan ƴan milkin mallaka suka saka ƴan ƙauyen nan da ƙarfi a makaranta, uwayensu dai basu san ba dalilin wannan. Dayawa sun gudu, wasu kuma sun tsaya hakanan dai ga sabon mahallin su. Nan da nan dai ganin cin nasarar ɗaliban nan na farko, uwayen da da ba su amince ba sun lura da muhimmancin da ke tare da saka yaransu makaranta. Idan suka dawo gida ran alhamis, da lokacin hutu, yaran masu gemu kamar yadda ake kiran su suna shan tattali kuma a hutar da su yin aikace aikace masu wuya.

Tare da sosuwar rai ne tsofin daliban nan goma suka komo bisa halinsu na ƴan makaranta. Zaman makarantar kwana, zaman mai wuya tare da jama’a, zaman horo mai tsanani, fada da abukan zaman, zuwa tabki, kuɗin da aka samu wurin uwaye da kuma ake rabawa da abokinsa, wasan zagaya, wasan ƙwallon ƙafa, kallon fim, abincin biki na lahadi, salla gidan mai geme etc…Fiye da abukai, tsofin ɗaliban makarantar mai gemu wato « mission » suna hulɗa sosai kamar dai ƴan uwa. Har a yau ma wannan ne ƙarfinsu.

Idan an karanta labarun nan masu ban sha’awa da umarni za a gane dalilin da ya sa har a yau, Michel Hamma Issa, Jean Maïdabo, François Daura Waho, Usman Dan-Lélé, Joseph Seydu Allakaye, Luc Maïdagi, Marc Elo, Karimu Jean-Marie Ambuta, Maïno Bétu, Serge Guero Bida, da abukansu duka na makarantar gidan mai geme suke riƙe da wannan igiya ta zumunci.

Labarai na ɗan littafin

La brochure, d’une trentaine de pages, traite les thèmes suivants :
Littafin mai shafi talatin yana magana bisa :

  • les premiers contacts avec les Pères Blancs et le recrutement,
  • hulɗ a ta farin tsakanin masu gemu da ɗaukar ƴan makaranta,
Le Père Sage rend visite au Baura Ganda Kassomou, 1954
Mai gemu Sage ya ziyarci Baura Ganda Kasomu, 3 ga watan december 1954
  • Isowa makaranta
  • Dangantaka tsakanin ɗalibai
  • adinin kirista
  • Dawowa gari da dangantaka da abukai da iyali
  • zuwa makaranta, zaman sana’a, sa kai
  • Tambayoyi game da adini da al’adu
  • Nijar nan gaba

Ya ƙare da shafi goma bisa halin rayuyar mutamen nan duka da ya ma tambayoyi.

Ana iya sauke littafin anan. Don samun littafin da aka buga, duba nan.

Antoine de Léocour

Antoine ya yi ziyara ta cuɗayyar juna tare da Tarbyya Tatali a Yamai da Dogon Dutsi lokacin bazara ta shekara 2008, wannan dai game da aikin shi na « master 2 » « Tafiya cikin duniya : ƙera huroje tare da haɗin gwiwa don ci gaba» a Poitiers. Lokacin ne ya rubuta shaidun nan goma na tsofin ɗaliban makarantar gidan mai geme wato « mission », wannan ne dalilin ƙirkira abin da ke cikin littafin.

Masoyin Afirka, ya dawo yin aiki a Nijar, amma ba a matsayin ƙungiyarmu ba cikin rani na shekara 2008, a matsayin ma’aikacin ONG ta duniya. Ya ci gaba da aiki a fanni jinsin ɗan Adam a Afirka ta tsakiya.

Antoine ya mutu saboda halbin bindiga da aka yi masa a kai kusa da iyakar Nijar da Mali ran 8 ga watan janairu 2011, Bayan kamawarsu jajibari da yamma a wani lafiyayyen gidan cin abinci a birnin Niamey mai sunan Tulusain, wannan dai aikin Al-Qaida ne. Yana da shekaru 25. Har yau ba a san Halayen ɗanye rasuwar Antoine de Léocour da na abokinsa Vincent Delory,da ya isko shi Nijar don armen sa. An sani dai sojojin Nijar sun nemi tsayar da motocin mahassada, amma sun samu rasuwar soja uku, Abubacar Amankaye, Abdallah Abubacar, da Abdu Alfari, sojojin Faransa ma sun sa hannu.

Antoine de Léocour

Tunawa da Vincent da Antoine

An girka allon kiftawar da tunawa da Vincent Delory da Antoine de Léocour ran Jumma’a, 21 ga watan Afrilu 2017 a filin mai suna “Jardin de l’Intendant de l’Hotel des Invalides a Paris », a gaban Sakataren mai kullawa da harkokin taimakon wandanda aka azabtar da, kuma gaban iyalansu da akukansu. An rubuta bisa allon:

Tunawa da Vincent Delory da Antoine de Léocour, wadanda suka mutu game da ta’addanci. Suna da shekaru 25 da haihuwa. Antoine da Vincent, abokai ne tun suna yara, ‘yan ta’ada sun kama su 7 ga watan Janairu 2011 a birnin Yamai, kasar Nijar. An kashe su washegari 8 ga watan Janairu 2011, a kasar Mali a lokacin da ake menan samun karshen garkuwa. Ba za mu manta da su ba.