Za a yin nunin ne kan rayuwar yau da kullun a filin wasa na makarantun karkarar gundumar Dankatsari: langa-langa, kokowa bisa kafa ɗaya, da gudu, wasannin hannu da raye-raye, kera abubuwan wasan yara, da kayan albarkatu na gida kamar su : karan gero, yumbu, a cikin bikin launuka.

Ayyukan AESCD wanda Ministan Turai da Harkokin Waje suka tallafawa.

Ranar da wurin nunin: daga 14 zuwa 28 ga Nuwamba 2019, A dakin médiathèque na Pont des Arts, Cesson-Sévigné, ranar Asabar, 30 ga Nuwamba 2019, a gidan unguwar Villejean (Rennes) a matsayin wani ɓangare na bikin Festisol (Festival des Solidarités .

A matsayin wani bangare na ayarin hadin kai, shekaru 10 na hadin kai tsakanin Cesson (Bretange) da Dankatsari (Dosso),

  • Satumba 2020 a Yamai - CCFN Jean Rouch: Alhamis 10 ga Satumba daga karfe 7 na yamma, nuni a zauren baje kolin jama’a. Kyauta ake shiga, Laraba 16 ga Satumba daga karfe 7 na yamma, ƙaddamar da vanyari, Babban ɗakin taro. Sai da Gayyata ake shiga.
  • Oktoba 2020 a Maradi- Alliance Française (buɗewa 10 ga watan Oktoba)
  • Nuwamba 2020 a Zinder - CCFN (buɗewa 4 ga watan Nuwamba)
  • Disamba 2020 a Agadez- Alliance Française (buɗewa, ba a sa rana ba tukuna)
  • Daga Maris 2021: Dogon Dutsi da Dankatsari tare da wani taron al’adu da wasanni

Shirye-shiryen da aka yi na farko an soke su soboda anobar bazarar Covid-19.