Idi Nuhu da Mamane Siradji Bakabe suka shirya wa Tarbiyya Tatali wannan bidiyon a shekarar 2018.

Takaitawa: ’Yan mata uku na kwalejin Dankatsari sun ƙuduri aniyar kammala karatunsu tare da samun difloma kuma su sami aiki mai kyau kafin yin aure. Daya dai ana neman a yi mata aure, abokanta biyu sun ƙarfafa ta kada ta yarda a yi mata aure. An yi amfani da ɗan littafin ’ Lafiyata da hakina na Matasa: Abin da ya Kamata in Sani - 637’ ’don bayyana abinda ake nufi da auren kananan yan mata.

Zazzage nan.

Ana amfani da fim ɗin don ayyukan ilimantarwa a Nijar da kuma a Faransa. An nuna shi a TV Saraunia a watan Oktoba shekarar 2020.

A matsayin wani bangare na ayarin hadin kai, shekaru 10 na hadin kai tsakanin Cesson (Bretange) da Dankatsari (Dosso),

  • CCFN Jean Ruch: Alhamis 10 ga watan Satumba daga karfe 7:00 na yamma, nuna wa jama’a a zauren baje kolin. Kyauta ake shiga, Laraba 16 ga watan Satumba a karfe 7 na yamma, ƙaddamar da vanyari, Babban ɗakin taro. Sai da Gayyata ake shiga.
  • Asabar 10 ga watan Oktoba 2020 a Maradi- Alliance Française
  • Laraba 4 ga watan Nuwamba 2020 a Zinder - CCFN
  • Disamba 2020 a Agadez- Alliance Française (ba a sa rana ba tukuna)
  • Daga Maris 2021: Dogon Dutsi da Dankatsari tare da taron al’adu da wasannin motsa jiki