Yau shekaru da yawa, ƴan makarankar Dogon Dutsi, tare da ban hannun malamansu suke ƙoƙarin adana gatannan gida masu alaƙa da al’adunsu.

Ƴan gatana maza da mata a makarantu

A cikin azuzuwan makarantu, ƴan gatanan unguwoyin Dogon Dutsi da na garuruwan kusa, tsohi uwayen iyali da yara, suna gabatar de gatanan hausa waɗanda su ma sun jiyo su ne a gida, da dare a lokacin gatana. Malaman makarantu suna fasara gatanan a cikin harshen faransanci, kuma ana rubuta wasu kalamomin da karin magana da hausa, san nan da faransanci. Ta haka ne tsarin tattara gatanan adabin baka ya samu shiga cikin tsarin aikin makarantun boko.

Amfanin gatannai cikin tsarin horo

A Nijar, gatana tana da mahimanci cikin horon yara. Don haka, kawo tsarin gatana a makarantun boko, kamar ƙarfafa horo da ba su tarbi’a na gari ne. Cikin gatannai, masali ana iya ganin inda ya kamata a ji tausayin maras ƙarfi, kar a yi wa wani mugun fata, kar a rena uwaye ko ƴaƴa, sai dai a yi masu biyayya, a riƙa jin maganar tsohi, a taimaki wanda ke cikin wahala, da sauran su.

A dalilin gatannan, ƴan makaranta ba su jin wata ɓaraka tsakanin makarantar da abubuwan gida, kuma yana sa su kama al’adunsu, kuma su san na wasu.

Misalai huɗu na gatannan Nijar

An tsamo su daga littattafanmu guda biyu.

Littattafanmu na gatannai : aikin taro ne

Aikin taro ne na ɗaruruwan mutane ;shi ya haifar da littattafanmu na gatannai, tun daga masu yin gatanan, zuwa malaman makarantar, har ƴan makarantar.

An buga fassalar farko a Faransanci, da Hausa da Zarma mai suna “A Makarantar gatannan Nijar” a Nijar a shekarar 2002 tare da taimakon kudade daga gungiyar taimako da shaidawa « aide et action ».
Daga nan ne aka buga littafin A makarantar gatannan Nijar a Faransa a watan Disambar 2004. Yanzu dai ya kare.

Kuna iya samun sabon littafinmu na gatannai mai suna ‘’il était une foi au Niger’’ ‘’Nijar, a wani lokaci can baya’’, a cikin kantinmu.

Kowa akwai irin aikin da ya yi : wani ɗan Nijar ya kula da zana hotuna, wasu malaman makaranta na Nijar da na faransa suka ƙara aikata matannai, kuma ya kula da tsara littafi.Gaisuwa ta masamman zuwa ga Nilo Royet saboda yin siffar littafin, zuwa ga Isufu M’barke da Dominique Berlio da suka rubuta matannan faransanci, da Saoude Ali Bida da ta fasara wasu matananan hausa zuwa faransanci. A yaɗa littafin a Fasansa da Nijar, kuma Tarbiyya tatali tana yin amfani da kuɗin sayar da shi ga ayyukanta na Dogon Dutsi.

La conteuse et le livre de contes