Fim wanda aka kirkira a cikin shekarar 2016 ta Idi Nouhou da Maman Siradji Bakabe a matsayin wani bangare na hadin gwiwa tsakanin Tarbiyya Tatali da B @ K TECHNO, wadanda suka samu tallafi daga Ma’aikatar DAECT mai
kulawa da Harkokin Waje a cikin garin Cesson Sévigné.

Takaitawa: Gaba daya rayuwar garin Lugu ta inganta ne ta hanyar samun ruwa. An rage wa mata ayyuka, ana ci gaba da yin tsabta, garuruwa sun falfado.
Zazzage nan.

An watsa fim ɗin a Lugu da Dankatsari kuma ana amfani da shi don ayyukan koyarwar ilimi a Faransa.

A matsayin wani bangare na ayarin hadin kai, shekaru 10 na hadin kai tsakanin Cesson (Bretange) da Dankatsari (Dosso),

  • CCFN Jean Ruch: Alhamis 10 ga watan Satumba daga karfe 7:00 na yamma, nuna wa jama’a a zauren baje kolin. Kyauta ake shiga, Laraba 16 ga watan Satumba a karfe 7 na yamma, ƙaddamar da vanyari, Babban ɗakin taro. Sai da Gayyata ake shiga.
  • Asabar 10 ga watan Oktoba 2020 a Maradi- Alliance Française
  • Laraba 4 ga watan Nuwamba 2020 a Zinder - CCFN
  • Disamba 2020 a Agadez- Alliance Française (ba a sa rana ba tukuna)
  • Daga Maris 2021: Dogon Dutsi da Dankatsari tare da taron al’adu da wasannin motsa jiki