Ƙungiyar Nijar ta Faransa ta tsara taron kwana biyu na al’adun Nijar a Paris a shekarar 2015 da 2016, Tarbiyya Tatali ta halarci taron tare da saida littattafai da hotuna. A shekarar 2017 an yi irin wannan taro amma Tarbiyya Tatali ba ta samu damar halartar taron ba.

A shekara ta 2018 an gudanar da taron ranar al’adu wanda ANIRE ya yi a Rennes. AECIN da AESCD suka halarci taron.

Tsarin ranar al’adun gargajiya na Nijar da na Bretagne

Asabar 23 ga watan yuni 2018

Wurin: Parc Gayeulles: santar professa Maurice Audin, 35700, Rennes

11H-11H30 Jawabi da gabatar da ANIRE, Gabatar da ƙungiyoyin da ake hulda da su.

11.30-12.30 Gabatar da Nijar, Taro, Tattaunawa

1:30 am - 3:30 am

  • 1- Tauttaunawa bisa kokawar gargajiya ta Nijar
  • 2- Aikin taron Langa-langa : mutane biyu suna fuskantar juna kuma suna tsayawa bisa kafa daya, wanda zai fi tsayawa da jumawa shi zai ci nasara
  • 3- Taron gabatar da kayan gargajiya
  • 4-Wrin dandanon abinci

16H - 17H gatana, tare da Rahina ta Nijar

Daga karfe 5 na yamma: dandanon dafuwa (gasasshen nama, tsire irin na Nijar, kopto (salatin ganye zogala), kilishi (busasshen nama), fari massa (fanke mai sukari), kenkena (fanke na garin wake), bissap (ruwan ganye jan huren yakuwa ).