An kammala wannan mataki.

Tarbiyya tatali tana shirya tarurrukan ƙara wa juma ilimi, kuma tana halartar mahawarori a Nijar da faransa, tare da abokan hulɗa. Ga misalai biyu.

Taron ƙarin sani bisa littafin ‘’Sarauniya da Lugu’’

Zaman taron ya haɗa mutane fiye da 120 a birnin yamai ; wani rukunin ƴan bincike ne kan fannoni daban daban, na jami’ar Abdu Mumuni ta yamai tare da ƙungiyar tarbiyya Tatali da kuma cibiyar al’adu ta hulɗar ƙasar faransa da Nijar cewa da ‘’Centre culturel franco-nigérien’’ suka tsara shi.
Akwai kuma Marie-Françoise Roy, shahararrar malamar ilimin lissafi ce, kuma ita take shugabancin sashen ƙungiyar a faransa, tare da Malam Bori zomo wanda yake shugabancin ƙungiyar a Dogon Dutsi, sun gabatar da littafinsu mai suna ‘’Lugu da Sarauniya’’ wanda yake ba dacikakkun bayanai bisa Lugu da Sarauniya a fannin rayuwarta, da al’adu, da tarihi, da kuma bisa fannin ci-gaban yankin.
Malam Mahaman Sa’adu, ƙwararren malamin jami’a ne a fannin ilimin kimiyya, shi ma ya ba da bayanai bisa halin binciken ilimin kimiyya da sani na gargagiiya.
Akwai kuma ‘’Atoinette Tidjani Alou’’ shahararrar malamar jami’a ce a fannin nazarin kwatanta adabi, kuma mambar wani rukunin bincike ce a fannin ilimin adabi, ta gabatar da wasu alamun da bincike ya ba da a Lugu da Bagaji, kan fannin bambancin jinsuna da manufofin ci gaba.
Alhada alkache’’, shahararren malamin jami’a ne a fannin ilimin tattalin arziki da shari’a, shi ya kula da tsarin gudanar da tattaunawar. Masu tattaunawar su ne, ‘’Boureima Alpha Gado’’, malamin jami’a ne a fannin ilimin tarihi, da malama ‘’Fatima Mounkaila’’ mai kula da tsarin ayyukan rukunin bincike a fannin adabi, da na jinsi da ayyukan ci- gaba .

Ƙasar ‘’Cadi’’. Binciken asuli

Wannan taron ƙarin ilimin, a tsara shi ta hanyar haɗin kan Tarbiyya Tatali da sashen ilimin kimiyya da ake ce ma ‘’Espace des sciences’’ a turance, ranar laraba, 3 ga watan nobamba 2004, a ‘’Espace ouest France’’ a Rennes.
Mai tafiyar da taron, malam ‘ ’Djimdoumalbaye Ahounta’’, ɗan ƙasar Cadi wanda ya binciko kakan-kakaninmu da ake kira’’ Toumaï’’ ; malamin ilimin kimiyya ne, kuma yana aiki a sashen cibiyar taimaka wa ayyukan bincike ta ƙasar ‘’Cadi ‘’mai tattara shaidodin halittun tarihi, da adana su, da kuma inganta su.
A cikin bayanan da aka bayar a taron, an taɓo zancen tawagar binciken da Michel Brunet ya jagoranta, wadda, a ranar 19 ga watan juli 2001, ta binciko shaidar rayuwar ‘’Toumaï’’ a keɓaɓɓen hilin bincike mai lamba 226 na cikin hamadar ‘’Cadi’’. Hakan ya ba da damar duba yadda irin wannan aikin binciken yake ci gaba, kuma da yadda sauran fannonin ilimin kimiyya suke taimakawa wajen inganta abubuwan nuna ire-iren halittu makamatan Ɗan Adam da suka rayu a bisa tsohon mulallin ƙasar ‘’Cadi’’.

Toumai
Toumaï