Wannan dai ya tara da al’adu da wasanni na gundumar Dankatsari (Nijar) don zaman lafiya da zamantakewa a farkon watan Maris na 2017: kiɗa, rawa, kokowa, gudu à kafa, a dawakai, bisa raƙuma, sana’ar aikin hannu da al’adun gargajiya ...
Wannan nuni an yi shi ne tare da hadin gwiwar AECIN da AESCD da taimakon Kudi na gidan Duniya na Rennes.
A matsayin wani bangare na ayarin hadin kai, shekaru 10 na hadin kai tsakanin Cesson (Bretange) da Dankatsari (Dosso),
- Satumba 2020 a Yamai - CCFN Jean Rouch: Alhamis 10 ga Satumba daga karfe 7 na yamma, nuni a zauren baje kolin jama’a. Kyauta ake shiga, Laraba 16 ga Satumba daga karfe 7 na yamma, ƙaddamar da vanyari, Babban ɗakin taro. Sai da Gayyata ake shiga.
- Oktoba 2020 a Maradi- Alliance Française (buɗewa 10 ga watan Oktoba)
- Nuwamba 2020 a Zinder - CCFN (buɗewa 4 ga watan Nuwamba)
- Disamba 2020 a Agadez- Alliance Française (buɗewa, ba a sa rana ba tukuna)
- Daga Maris 2021: Dogon Dutsi da Dankatsari tare da wani taron al’adu da wasanni
Shirye-shiryen da aka yi na farko an soke su soboda anobar bazarar Covid-19.
