“Akwai Magana! Za mu yi magana game da shi (Season na 2)" jerin zane-zane guda huɗu ne da aka yi fim a shekarar 2023 a matsayin wani ɓangare na ayyukan ƙungiyoyin AESCD, AECIN, RAEDD da Nuvel Espoir don yancin mata da ’yan mata.

Jigogi

Alichina Allakaye, Bawa Kadade Riba da Mahamat Ado Saleh ne suka yi rubutun, sai Arice Siapi ta yi jagorancin, sun shafi jigogi kamar haka: zabin mijin ko matar aure, cikin da ba a so dauka ba, hailar farko da tashin hankalin iyali.

ZABIN ZAGANI/LE CHOIX DE ZAGANI.
Mahaifin Zagani yana son ya aurar da ita ga dan kokawa amma ba zabinta ba ne. Mahaifiyarta da babarta sun shawo kan uban ya hakura. Ana iya ganin fim ɗin a nan, rage sigar nan.

MIGUN GAMO/MAUVAISE RENCONTRE
Zinaria ’yar makaranta ce kuma wani mugun yaro yana son lalata da ita. Ta yi ciki ba da son ta ba. Zanariya za ta ci gaba da karatunta? Ana iya ganin fim ɗin a nan.
nan, rage sigar [nan>https://vimeo.com/805970106].

ALDA/LES REGLES
Ubeida ta tafi aji da ciwon ciki. Ba ta iya maganar haila da mahaifiyarta. Amma Babarta ta zo ta taya su magana bisa haila. Ana iya ganin fim ɗin a nan, rage sigar nan.

ARADU BABA TAHE/ATTENTION PAPA ARRIVE
Sakaka miji da uba ne mai fushi, mai tashin hankali ko da yaushe. Matarsa ​​da ’yarsa sun fake wurin maƙwabcinsu. Maƙwabcin ya ja hankalin shi. Ana iya ganin fim ɗin nan, rage sigar [nan>https://vimeo.com/805969628].