Ƙungiyar ƴan Faransa ce da aka kafa a ranar 13 ga watan Maris 2009.
Burinsa shi ne:
a) inganta hadin kai da mu’amala tsakanin al’ummar kananan hukumomin Cesson-Sévigne da Dankatsari, sashen Dogon Dutsi (Nijar), musamman a fannonin ilimi, horarwa, lafiyar mata da yara, samun damar yin amfani da ruwa, da tsaftar muhalli, da samar da abinci da tallafawa shirye-shiryen tattalin arziki da musayar sana’o’i da al’adu,
b) da tsoma hannu cikin harakokin ƙungiya a Cesson, tare da bunƙasa ayyukan horo, da yaɗa labaru bisa abubuwan da ake zartarwa a Ɗankatsari, kuma a Nijar baki ɗaya.
Garin Cesson ya ba AESCD aikin gani soye da soye na hulda gani a kasa tsakanin Cesson da Dankasari a farko na shekara 3, daga 2009 zuwa 2023. Tsakanin 2018 zuwa 2020, an sanya hannu bisa yarjejeniyar tsakanin AESCD da garin Cesson-Sevigne, an sake sabunta ta don 2021-2023.
AESCD tana shiga cikin dandalin hadin kan kasa da kasa na Cesson musamman wajen shirya “Festival of Solidarity-> 332] sannan kuma tana tsoma baki cikin harakokin makarantu na Cesson.
Ku shiga ƙungiyar AESCD ! ku goya mata baya !
Adareshi :
AESCD Tarbiyya Tatali
C/O Jean-Jacques Nevanen
18 rue de la Rabine
35510 Cesson-Sévigné
Talho : 02 99 83 81 01
Mel : aescd@tarbiyya-tatali.org