Sha’idodin da aka gudanar da kuɗin garin Cesson-Sévigné ko kuma waɗanda aka gudanar da haɗin gwiwar garin Cesson - Sévigné

Ana kashe kudi wajen aiwatar da ayyukan tallafin garin Cesson-Sevigne kamar wajen :

  • ayyuka masu haɓaka ’yancin mata da lafiyar su,
  • bunƙasa tattalin arziƙi da ƙananan bashi don inganta ayyukan samar da kuɗaɗen shiga,
    - wajen horo.

Tsarin aikin 2019 yana da abubuwa biyu

Tsarin aikin 2020 yana da abubuwa biyu

  • micro-credit ga mata wandanda suka iya karatu da rubutu a Tunzurawa (kungiyar Alheri) da Gofawa (kungiyar Hadin-Guiwa) da kuma karfafa kudade bashi a Kamrey (kungiyar Tchigaba) da Dogontapki (kungiyar Niyya)
  • gudummawa wajen wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana Hadakar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Karki Malam (hada-hadar kudade ta SDE35)

Aikace-aikacen da wasu abokan hulɗa suka yi

Ban da ayyukan tsari , an samu kudaden yin wasu ayyuka a 2018

  • a Kotun shawara na Département na 35 don ilimin jima’i na ’yan mata da kuma yakin auren ‘yan mata ƙanana,
  • a Rennes Métropole a fagen tsabtacewar dakunan lafiya.

Tsarin aikin " Abubuwan inganta ci gaba” Ma’aikatar Harkokin Waje, da Yankin Bretagne, da SDE35, da CEBR, da AELB da CD35 sun amince da a ci gaba da yin abubuwan inganta rayuwa a ƙauyukan Dankatsari 2019-2020" ( ci gaban tsarin aikin 2017-2018).

Ayyukan dai za su mayar da hankali kan fannoni kamar :

  • ODD6: kulawa da samun ruwa : horo na CGPE (kwamitoci masu kulawa da samun ruwa), da AUSPE (kungiyar Masu amfani da Ruwa) da kuma masu gyare gyare a garin, da masu gyaran wurin samun ruwa goma sha biyu da rijiyoyi goma sha biyu, da kafa karamin AEP na garuruwa da dama a Kandadame.
  • ODD6 Tsarin tsabta : Gina wuraren bayan gida da wuraren wanka na gidagen kiwon lafiya guda shida, da gina salangogi shida a makarantu
  • ODD2, ODD15 Gyaran wurin sa kayan lambu na Marake Rogo da kafa pompo mai aiki da rana, horon masu aikin lambu, da na gandun lambun ma’aikatar magajin gari da kuma lambun makaranta.
  • ODD7 Makamashi: kafa kaya masu aiki da hasken rana na wuraren kiwon lafiya guda shida
  • ODD5, ODD1,0DD3: horar da ungozomai, horar da mata da maza a tsarin iyali a cikin kauyuka, horon kungiyoyin masu karatun yaki da jahilci, samun kananan bashi don mata masu karatun yaki da jahilci, tallafi ga SCOFI (makarantar ’yan mata).
  • ODD4: kafa kayan aikin kamar teburori.
  • ODD16, ODD2, ODD5 Taimakawa ma’aikatar magajin gari, wajen samun takardun daban daban, da kuma karbar kudaden haraji.

Taimako na mahimmanci zai fito ne daga kasar Nijer (kashi 35% na kasafin kudin) da kuma mutamen yankin.

17 Manufa don Canza Duniyar mu