RAEDD na daya daga cikin masu tsare-tsare 11 da aka zaba, cikin jimillar 330 masu neman taimako, wajen asusun PISCCA (sabin ayyukan kungiyoyin farar hula da hadin gwiwar masu aiwatar da ayyukan ) na ofishin jakadancin Faransa a Nijar a shekarar 2022.
Manufar aikin da sakamakon da ake tsammani
A sashen Dogondouchi, barin makaranta ya yi yawa kuma ya fi shafar yara mata.
Dalilan suna da yawa kuma sun shafi aure da wuri, daukar ciki da wuri, nesantar yanki, talauci da rashin isassun tsarin makaranta. Haka kuma kebe su ko watsi da karatunsu na da nasaba da wahalar da suke da ita wajen tafiyar da tsaftar jinin haila da lafiyar jima’i, abubuwa ne da ba ahira bisan su, shi yake sa ‘yan mata yi asara idan suka fuskanci matsalolinsu a lokacin samartaka.
Makasudin wannan aikin shine, ƙarfafa ci gaba da karatun ƴan matan sakandare na kwalejoji 16 a cikin Sashen Dogondutsi
Kamar
- Horar da malamai iyaye mata hudu waɗanda za su kasance masu baiwa ƴan matan kwaleji shawara don taimaka musu wajen matsalolinsu.
- Ƙarfafa tsafta da amincin ɗaliban makarantar sakandare, musamman taimaka wa ƴan mata na sakandare damar yi hailarsu lafiya. ‘Yan mata 2,550 ne za a horawa wajen kula da tsaftar jinin haila, gujewa aure da wuri da kuma guje wa juna biyun kafin aure. Salangogi da wuraren wanke hannuwa za su kasance masu aiki don samar da ingantaccen tsaro.
- Haɓaka ilimin ɗaliban sakandare game da lafiyarsu da haƙƙoƙinsu a matsayin matasa. Ana bawa kwalejoji ƙasidu “Lafiyata da haƙƙina a matsayina na matashi” kuma an horar da malamai game da yin amfani da ƙasidar.
Tsarin ayyukan
Matakin ya gudana ne a kwalejojin karkara 16 a cikin kananan hukumomi 6 na sashen Dogondutsi na yankin Dosso.
- Karamar Hukumar Dankatsari: a kauyukan Gubey, Dankatsari, Bawada Guida, Bawada Dagi
- Karamar Hukumar Dogondutsi: a kauyukan Togone, Rigia Samna, Kuka Bakoye, Kalgo.
- Karamar Hukumar Dogonkiria: a kauyukan Issakitchi, Bugu
- Karamar Hukumar Kieche: a ƙauyen Rey Rey
- Karamar Hukumar Matankari: a kauyukan Bagagi, Salga, Matankari
- Karamar Hukumar Sucocutane: a cikin kauyukan Dubalma, Kururube Dakau.
Ga ayyukan da aka shirya
- Horar da malamai mata a Dogonduchi wadanda za su yi aiki a matsayin masu baiwa matasa shawarwaru. Na tsawon kwanaki 2 wannan horon zai kunshi batutuwan da suka shafi tsaftar jinin haila, hana daukar ciki, hana aure da wuri da daukar ciki ba aure, abin da ya kamata a yi idan an samu juna biyu, rigakafin cin zarafi, da jawaban da za a yi wa ’yan mata da samari. Manajan kula da kimantawa na kungiyar RAEDD zai jagoranci horon, tare da mai kula da ilimin ’yan mata na ma’aikatar sakandare na sashen Duchi, da mai kula da lafiyar haihuwa ta gundumar Dogonduchi.
- Ayarin wayar da kan jama’a game da kula da tsaftar jinin haila, ƙwayoyin hana daukar ciki, aure da wuri da daukar cikin da ba a so. Za a shirya ayarin ne a kowane kwalejoji 16 tare da jagoranci ta tattaunawa na wadanda aka hora su 4, wato cibiyar kiwon lafiya, cibiyar kula da jama’a, wani ma’aikacin RAEDD da kuma mai kula da makarantun yara mata ta Dogonduchi.
- Kyautar kayan aikin tsaftar al’ada wanda ya kunshi kananan wanduna 4, adibas na tsafta 4 da jaka da CSO Kijima Kinaja ta bayar zuwa ga ’yan mata 2,550 na kwalejojin karkara 16 na Dogondutsi
- Sa ido kan yadda ake amfani da salangogi da RAEDD ta riga ta gina, musamman dangane da matsalolin haila. Za a tabbatar da shi, yayin ziyarorin da aka tsara, tare da haɗin gwiwar ma’aikatan cibiyoyin ilimi da membobin COGES. Wannan sa ido zai kuma shafi bin ka’idojin tsabta da za a kiyaye: tsaftacewa, kafa na’urorin wanke hannu da sabulu.
- Karfafa ilimin yaran makaranta game da lafiyarsu da hakkokinsu a matsayinsu na matasa, za a rarraba kasida “Lafiyata da hakkokina a matsayina na matashi, abin da nake bukata in sani” a kwalejoji 16 na aikin, kowannensu yana da littattafai 30 a ɗakin littattafai. . Dalibai da malamai za su iya aiki da shi. Makarantar za a ba amana kulawa da su.
- Koyarwa kan amfani da kasida ga malamai 16 na ilimin rayuwa da na duniya da malamai 16 na ilimin iyali na kwalejojin da aikin ya shafa, da kuma wakilai 16 na tsarin kiwon lafiya da ke da alaƙa da waɗannan kwalejoji.
An tsara aikin na tsawon watanni 6, tsakanin Nuwamba 2022 da Afrilu 2023.
Tallafin haɗin gwiwa ya fito ne daga AECIN da AESCD da kuma kwamitocin gudanarwa na cibiyoyin da abin ya shafa.