Tun daga shekara ta 2009, an dasa bishiyoyi dubu arba’in a ƙauyen Dankatsari albarkacin haɗin gwiwa tsakanin Cesson Dankatsari ., a cikin cibiyoyin na wuraren jama’a (kasuwanni, makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya) ko kuma mutane sun dasa a cikin gidajen su ko gonakin su.

An fi dasa akwara, zogalen, dogon yaro da kuka.
Ana amfani da itacen akwara don yin alamar iyakokin filaye da wuraren kiwo, wanda ke iyakance rikici tsakanin masu kerawa a cikin sarrafar ƙasa. Tana ba da jire

Zogala icce ne mai saurin tsiro, har a cikin bushashun yankuna, ganyenta na da amfanin sosai wajen ginin lafiyar jiki.
Saida jire da ganyen zogale na sa mutume su samu kuɗi.

Wani garken zogala kuma za a hada shi da lambun an makarantar da aka girka a wani gari na kwamin ɗin Matankari, tare da taimakon gidauniyar Total.

Ana ta ci gaba da ɗaukar matakin kowace shekara a kwamin ɗin Dankatsari.
A cikin shekarar 2019, tsire-tsire 10,000 ne aka samu a garke biyu.
A cikin ƙauyen Dankatsari shuke-shuke 6000:

  • akwara shuke-shuke 3000,
  • Zogala: tsire-tsire 1000,
  • Dogon yaro: tsire-tsire 1000,
  • Kuka : tsire-tsire 1000.

A ƙauyen Marake-Rogo: tsire-tsire 4,000

  • akwara tsire-tsire 3000
  • zogala: tsire-tsire 1000.