Kudin ma’aikatar harkokin waje ta Faransa ta sa an samu aiwatar da aikin rahotannin tsare-tasre a Dankatsari.

  • A fagen aikin samun ruwa : Gyara da kafa kayan aiki, horon kwamitocin masu gyare gyaren ci gaba da bunƙasa salangai (latrines)
  • Don bankunan da injin niƙa hatsi: kyautata kayan aiki, shirin horon, jerin kauyukan da za a kai wa kaya
  • Don aikin lambu, an keɓe yankuna goma sha ɗaya kusan tabkuna
  • Don kiwo, an fi ba da karfi wajen alluran kiwon lafiyar dabbobi, inganta wuraren samun ruwa na dabbobi, da ɓunkasa kiwo kaji

Ayyukan hulɗar garin Cesson-Dankastari na dogare ne a kan shawarwarin wannan nazarin.

Waɗannan nazarorin na ba hukumomi damar bayyana da yin ayyuka da sauri idan abokan hulɗa sun tuntuɓe su.