Yanaya da guri
Garuruwan gundumar Dankatsari ba su da lantarkin ma’aikatar NIGELEC. Kuma suna da bukatu dayawa.Abubuwan samun lantarki su ne kamar haka : injin jenarato, batir din zahin rana.
Gurin ‘bunkasar da samun lantarki domin kasancewar anfanin na masaman shi ne samun magudan kudin kafin a sami abubuwan da za’a taimakawa domin datatar hagna ta kulawa.
Masamancin gaugawa farko
Kokowa ita ce samar da hasken lantarki cikin ma’aikatun barikin Dankatsari. Garin Dankatsari ya kasance samun bukatar a zo a gani don samun kaya aikin da suka dace kamar haka : su ne fanhon murtsatse da kotamtatiyar pampo da ke aiki da na’ura zahin rana da injin generato .
Ma’aikatu datatu su ne kamar haka :
- Ruwa : jan ruwa ko samar da ruwan wuni kamar awa 15 don samun issashen ruwa na 75 m3 mai kotamcin karhin gudar pampo kamar 5m3 ga awa ; awar 5 ko wane dare
- Gidan likitan : rayarda akwacin sanyi, panka a kayan aikin likita da samun hasken lantarki cikin dare kotamcin awa uku ko ga dakin ceton gaugawa
- Lakol : haskawa kambacin awa ukku da dare
- Injin nikan hatsi : da rana
- Samar da lantarki ga injin mai kokkolwa da kingin su, cajin batir din salulla da rana ko awa ukku da dare
Himma ko aiki na farko
Lokacin ziyarar magajin Garin Dankatsari a Cesson a watan novembar 2013 gurinsa biyu ne, na farko su ne :
- Sammun hasken lantarki ga lakkol shaidadda ta garin don ranar bukin tanada shekara 50 a alip 2014
- Samar da hasken rana a gidan likita (haske, akwatin sanyi, inji mai kokkolwa na’ura) inda koraran likita na gudumar yake
Samun kuɗi : haduwar concil na ma’saman na matasarin, samar da kuɗin garin Cesson, talahwar doka Oudin da SDE 35 da talahwar gundumar Dankatsari
Duka kayan aiki biyu nan an kammala su a shekarar 2015.
Samun kayan aiki a fanin makamashi na Bawada Dagi da Gofawa
Ya shafi kafawar dandalin aiki biyu ; ɗaya a ƙauyen Gofawa, wanda kamfanin Energy Union 35 da AESCD suka ba da tallafi, na biyun kuma a ƙauye Bawade Dagi, wanda Gwamnatin Nijar ta yi.
Dandalin aiki Gofawa, wanda wani Kamfanin Dogondutsi ya yi, na ban sha’awa, tun da ya hada da janareta wanda ya kaddamar da injiniya. Yana da mahimmanciyar ta’aziyya da aminci ga masu amfani, wato inda za a tada shi, wani ɗan button ake turawa.
Wannan dandalin mai ban sha’awa yana ba da damar a yi la’akari da ƙirƙirar ƙaramar cibiyar sadarwa a ƙauyen.
Kayan aiki na Cibiyoyin Kiwon Lafiya Uku
A shekara ta 2016-2017, sauran gidaje uku na kiwon lafiya na kwamun ɗin Dankatsari, da kauyukan Gubeye, Bawada Guida da Ruda Gumondaye, sun samu kayan aiki, game da samun wasu kudade daga kungiyar makamashi wato Syndical de l’Energie 35, na garin Cesson da kuma taimakon AESCD.
Karshen shekara ta 2018, an sa wa sabuwar asibitin Dankatsari, da ke kusa da gidan likita, lantarki na zahin rana, an samu yin sa ne da kudade kyngiyar Energy 35, ta garin Cesson da na AESCD.
A farkon shekarar 2020, an kafa kayan aiki masu tafiya da makamashin hasken rana a Cibiyar lafiyar garin Gofawa da dakuna lafiya biyu na Bawada Dagi da Dogontapki tare da samun sabon taimakon kudi wurin kungiyar lamtarki mai sunan Syndical de l’Energie 35, daga garin Cesson, da yankin Bretagne da kuma kudaden AESCD. An yi wa wani Mai aikin lantarki na Dankatsari horo akan aiki da lantarkin hasken rana ta hanyar lura da yadda wani mutumin Yamai ya yi kafawar.
A karshen shekarar 2020, Cibiyar Hadakar Kiwon Lafiya ta Karki Malam da dakunan lafiya guda biyu na Kaura Lahama da Kamrey aka kafa wa makamashin hasken rana sakamakon wasu kudade da aka samu daga kamfanin Syndical de l’Energie 35, na garin Cesson, na Yankin Bretagne da kuma kudaden AESCD.
Kwanan nan an sanya ƙarin layin da ke ba da izinin cajin wayoyin hannu a Kaura Lahama, Kamrey da Karki Malam.
A farkon shekarar 2022, an gudanar da na’urorin kiwon lafiya na Saurin Kaihi, Duzu da Kore Gabass, tare da sanya karin layin da za a yi cajin wayoyin salula a wasu cibiyoyin kiwon lafiya guda biyar da aka riga aka kafa masu abun samun watar rana a Gofawa, Ruda Gumandey, Dogontapki, Bawada Guida and Gubey. Za a tsarar da horon ma’aikatan da COGES don kula da kayan aiki.
Kafa fitulun hasken rana a kauye guda don goji
Kafa tashoshi hudu na caji da fitulun hasken rana dari da sittin, a karkashin nauyin yara, don inganta iyalai a kauyen Ruda Goumandey, Lama Foundation da SDE35.
