Fim “’Yan mata uku a Dankatsari” an watsa shi akai-akai a Faransa, musamman a cikin kwalejoji na Cesson da na kewaye da Rennes.
Muna so mu yada shi a cikin Nijar, musamman a cikin ƙauyukan Dankatsari.
A talabijin na Nijar
Darektocin fim din Idi Nuhu da Saradji Bakabe sun sami watsa shi kyauta a gidan talabijin na Nijar. . An watsa shi a TV Saraunia a watan Oktoba 2020.
A kwalejojin Dankatsari
Tare da goyan bayan Gundumar Ille et Vilaine, an yi watsa fim ɗin “‘yan mata uku a Dankatsari” a kwalejojin gundumar Dankatsari.
Kungiyar ta ƙunshi daraktocin biyu na fim din Idi Nouhou da Saradji Bakabe, da shugaban haɗin gwiwa Cesson-Dankatsari na RAEDD da Malama Issa Aïchatou Da Badio Doka, [shugabar SCOFI- > 680] (Zuwa makarantar ’yan mata) a Sashen Dogonduci.
An yi gwaje-gwaje fim din a kwalejoji shida na Gubeye, Bawadi Daji, Dankatsari, Kamrey, Dogon Tapki da Bawada Gida. Kuma dalibai 541, cikin su ‘yan mata 307 da kuma maza 234, sun kalli fim din. A Dankatsari, yawan la’akarin masu kallon, ya sa dole a ka yi fim din saw biyu ‘yam mata 103 da maza 95, don zaman darussan da tattamnawa, da manyan jarumai uku na fim: Umalher Chaïbu da Zeïnab Hamidu. Ta ukun Zeïnab Alio Chanu tana karatu a Malbaza. An sami kuma halartar membobi biyu na ƙungiyar iyaye ‘yan makaranta.
An samu matsaloli wuri wasa fim din saboda rishin kayan aiki. Ana bukatar janareta, da abun watsa fim, don fim ɗin yana kan kwamfuta. Amma azuzuwan zana sun yi haske sosai, kuma sau da yawa abun watsa fim din ya ki yin aiki dole aka duba fim din kai tsaye akan kwamfuta.
Bayan kowane nuni fim din, shugaban RAEDD, da Issa Dan-Badio Doka da Idi Nuhu suke daukar lokaci don yin muhawara da / ko bayyana wasu bangarorin fim din. Issa Dan-Badio Doka tana kara yin bayani kan amfanin karatun ’yan mata da daukar misalin kanta. Ta kara tuna wa jama’a rawar da maza ya kamta su taka wajen taimakon ’yan uwansu mata ta hanyar fahintar da iyayensu kada su yi wa ‘yan mata aure da wuri.
A yayin muhawarar, ɗalibai sun nuna cewa sun fahimci cewa babban batun shine auren dole da ake yi wa ‘yan mata kanana. Daliban, mata har ma mazan, suna tunatar da hujjojin da haruffin ɗaya ya bayar don ƙin auren dole na kananan mata : yawan aiki, wanki, dafe dafen abinci da ba ta ci ma watarana, aikin neman ruwa, da sauransu.
Ga tambayar: "Me ya sa ba ki son yin auren dole ? Yawancin ‘yan mata kanana suna cewa saboda kamar:
- Wulakancin miji a cikin lamarin auren da shi kansa lallai bai yarda da shi ba;
- Tsaida karatun yarinya ba da son ta ba ;
- Bata rayuwa ...
Banda Dankatsari, ‘yan mata ba su sa baki ba cikin hirar kamar maza. Sai da malama Issa Aïchatou Dan-Badio Doka ta ɗauki magana, ta tambaye su idan sun amince da maza sun fi su ne don su dauki magana.
An yi maganar wasu auren dole :
- A Goubey, yarinya ta kasance mai karatu sosai tana da matsakaici 14. Iyayenta sun aurar da ita ga wani saurayi da ke zaune a Loga. Wata budurwa kuma ta kai karar iyayenta wajen hukumomi saboda suna so su yi mata auren dole alhali akwai wanda take so.
- A Dogon Tapki, an yi wa wata daliba auren dole, amma bayan mako guda kawai auren ya mutu.
Ga shawarwarin malaman makarantu :
- A yi ta nunin fim din ga jama’ar Dankatsari, don a garin ne aka yi tsarin shi.
- A yi ta nunin fim din cikin wasu ƙauyukan gundumar Dankatsari, saboda a can an fi samun matsalar auren dole sosai.
- A tsara cikin shekarar taro biyu game da bayanni bisa auren dole wajen iyayen daliban a cikin ƙauyuka, don ƙarfafa saƙon.
A makarantun firamare a Dankatsari
An shirya nunawa a watan Yunin 2020 a makarantun firamare a Chanono, Tullaye; Tugana peul, Jigarwey, Danzure, Kolfa 1, Nakigaza, Sarkin ruafi, Kamrey peul Tunzurawa a matsayin wani ɓangare na tallafawa ilimin yara mata.