A matsayin wani bangare na haɗin kai Cesson-Dankatsari, an tsara shirin samun ruwa a duk yankin karkarar Dankatsari, sakamakon kuɗade daga Cesson karkashin dokar Udin-Santini kuma da sauran abokan tarayya da yawa (Jihar Nijar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa, Tsibiyar ruwa ta Loire-Bretagne, ƙungiyar ruwa ta Basin Rennais).
Gwamnatin Nijar ce ke ɗaukar alhakin kafa sabbin kayan aiki, kamar karamin pompo na garuruwa ko rijiyoyi.

Kudaden da aka tara a Faransa sun ba da damar sake gyara kayan aikin da ake dasu: samar da ruwan sha masu tsabta (AEP), rijiyoyin. Akwai tsarin horo da ake yi lokacin da ake waɗannan gyare gyaren.
An kafa wa kowace rijiyar, Kwamitin Gudanar da ayyukan samun ruwa (CGPE), wanda membobinta kuma sun sami horo a can baya. CGPE ta ƙunshi mutane 5: shugabanta, sakatare, mai baitul mali da masu tsafta biyu waɗanda ke da alhakin tsabtata maɓallin ruwan, kuma galibin su mata ne.

A farkon shekarar 2014, shirin horo ya ƙunshi CGPEs 35 na mutane 5, koyaushe cikinsu da aƙalla mata biyu. A yayin zaman horo na kwanaki 4, ana gabatar da doka mai amfani, ka’idojin kyakkyawan wurin sarrafa ruwa da kayan aikin da za’a aiwatar. Wannan shirin horarwar ya ci gaba da sabbin CGPE guda 20 a farkon shekarar 2015, sabbin CGPEs 30 a karshen shekarar 2016. A karshen shekarar 2018, an kafa zaman horon ne ga masu tsafta 170 da kuma ma’aji 85. A farkon shekarar 2020, an horar da sababbin CGPEs 24.
Bugu da kari, a farkon shekarar 2020, don tallafawa girka ko gyara kananan AEP da wuraren ruwa, an horar da mambobi 60 na ƙungiyoyin Masu Amfani da Ruwan Jama’a (AUSPE).

Sauran ƙungiyoyin suna samun horo, kamar masu gyara biyu a kowane ƙauye da aka yi horon ‘yan CGPEs: a watan Yunin shekarar 2015, rukuni biyar, kowace mai mutane 22 masu gyara a ƙauyuka, sannan a farkon shekarar 2017 rukunoni uku na masu gyaran 20 kowane, kuma a ƙarshe masu gyara 72 a cikin shekarar 2019 zuwa farkon shekarar 2020. Wanda duk aka hora sai a ba shi kayan aiki.
A Goriba (kwomin ɗin Matankari) da Birbiro (kwomin ɗin Dogonkiria), AUSPE da CGPE suma an horar da su.

A shekarar 2020-2021, a garin Dankatsari, an shirya horar da kwararrun ’yan gyara guda biyar wadanda tuni aka tantance sannan kuma aka tsara horar da mambobi 90 na ƙungiyar CGPE ko AUSPE.   

A farkon shekarar 2022, a garin Dankatsari, an gudanar da wani horo na kwanaki uku ga mambobi 90 na kungiyar CGPE ko AUSPE, a rukuni uku na mutane 30. An gudanar da horo na tsawon mako guda ga kwararrun masu gyaran gyare-gyare guda biyar wadanda aka ba su kayan aiki kuma suka zo gyara rijiyoyin lokacin da CGPEs ta tambaye su.