Ci gaba mai dorewa a ƙauyukan Dankatsari: makamashi, muhalli, tsafta, tallafawa mata, ƙarfafa ayyukan karamar hukuma

Ma’aikatar Turai da Harkokin Kasashen Waje (MEAE) tana tallafawa wannan aikin, a matsayin wani bangare na goyon bayan hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, na ayyukan shekaru biyu, cikin tsawon lokacin 2020-2021.

A Dankatsari, makasudin aikin shi ne ci gaba mai dorewa ga dukkanin mazaunan kauyukan, musamman mata da matasa, ta hanyar aiwatar da matakai da dama. Babban sakamakon da ake tsammani shi ne karfafa ayyukan hukumomin birni a cikin makamashi da muhalli, kafa aikin horo da dama, inganta kayan aikin kiwon lafiya a cikin hasken rana da salangogi, karfafa ikon samun cin kan mata ta hanyar tsarin iyali, duka suna ba da muhimmiyar ci gaba a Dankatsari.

A Ceson-Sevigne, manyan wadanda suka ci ribar su ne ɗaliban firamare da na sakandare da ke amfani da horon ilimi, da na zaman ɗan ƙasa da rayuwar al’umma ta hanyar da ta dace game da rayuwa a Dankatsari (tsoma baki a ajujuwa) da musayar takardu a makarantu.

A takaice za a aiwatar da ayyuka kamar

  • Dangane da makamashi: haɓaka tsarin birni ta hanyar lissafi da nazarin buƙatu, kayan wutar lantarki masu amfani da hasken rana don tsarin kiwon lafiya a gidajen lafiya 5.
  • Dangane da muhalli, wadatar abinci da tsaftar muhalli: horo kan karfafa kasa don samun albarka sosai inda aka yi subka, wuraren yin subke-subke, horar da masu lambuna, girkawa da kulawa da salangogi a tsarin kiwon lafiya 6 da makarantun 14.
  • Dangane da karfafa wa mata da ’yan mata da inganta kiwon lafiyar mata da yara game da samun : kananan basusuka, horo a fanin ilimi, tsarin iyali, tallafa wa ilimin yara mata.
  • Karfafa ayyukan karamar hukuma: wayar da kan mutane game da mahimmancin haraji da yin takardun aifuwa, tallafa wa bankunan hatsi huɗu da kwaleji.
  • Sadawa kan sakamakon da aka samu, a Nijar da Faransa.
  • Kulawa da ayyuka a kai a kai.

Kungiyar MEAE, da jihar Nijar, da garin Cesson, da Rennes Métropole, da SDE35, da yankin Bretagne da kuma AESCD ne suka dauki nauyin aikin.