Ayyukan da suka sami tallafin kuɗaɗe Cessson-Sévigné ita kadai ko tare da wasu abonkan aiki

Sun hafi yankuna kamar :

  • ayyuka masu haɓaka ’yancin mata da lafiyar su,
  • bunƙasa tattalin arziƙi da ƙananan bashi don inganta ayyukan samar da kuɗaɗen masu shiga,
  • horo.

Tsarin aiki na 2021 yana kumshe da abubuwa biyu

Ayyukan 2022 da 2023 za’a yanke hukunci ta hanyar yarjejeniya tsakanin ƙananan hukumomin Dankatsari da Cesson-Sevigne.

Ayyukan da wasu abokan tarayya ke ɗaukar nauyi

“Tsarin”Ayyukan haɗin kai don ci gaba mai ɗorewa na ƙauyukan Dankatsari" (wajen ci gaba da tsarin aikin 2018-2020) ya sami karbuwa daga Yankin Bretagne. Tana samun karuwar kuɗi daga Cesson-Sévigné, Rennes Métropole da MEAE (na 2021).

Ayyukan za su mai da hankali kan abubuwan kamar

  • Karfafa karfi: kwarewar abokan tarayyar Nijar (zababbun jami’ai, ma’aikatan birni, mambobin RAEDD da sauran kungiyoyi na cikin gida) na tsarin bayanan kasa wanda zai ba da damar sanya ido kan aikin da goyon bayan yanke shawara, tallafi ga matsayin jama’a da biya haraji.
  • Muhalli: horarwa kan taimakawa sake farfado kasar noma, sake dasa itatuwa
  • Kiwon lafiya: samarda bukkoki na kiwon lafiya da hasken rana, inganta kayan aiki wajan samarda kayan kiwon lafiya a baya, samarda bukkoki na kiwon lafiya da bandakuna (dakuna biyu da na wanka), horar da kwamitocin gudanarwa na tsarin kiwon lafiya wajen kula da kayan lantarki da tsafta, horar da ungozomai
  • Ilimin karatu da tsarin iyali: horon koyon karatu ga mata rukuni biyu, aikin wayar da kai na wata mai kula da tsara iyali, horar da wadanda za su ba da horo maza da mata don tsarin iyali, karfafa horo ga mataimakan maza da mata da aka horar a baya, kayan aikin fadakarwa na ci gaba
  • Taimakawa harkar tattalin arziƙin mata: ƙaramin bashi ga mata wadanda suka iya karatu da rubutu, bunƙasa kiwon iyali da samar da amalanke don amfanin ungozomai
  • Tallafawa wajen ilimi, musamman ga diya mata: ofishin jakadancin na birni ke kula da shi a makarantun da mata kaɗan ke ciki, horarwa akan amfani da ƙasidar “lafiyata da yancin matasa”

SDE35, CEBR da AELB5 sun amince da wasu abubuwan haɗin gwiwa dangane da samun makamashi, ruwa da tsafta. Ana tsammanin gudummawa mai tsoka daga jihar Nijar (kashi 35% na kasafin kuɗi) da kuma jama’ar gari.

Manufofin 17 don canza duniyarmu