An kammala wannan mataki.

A cikin wannan shafin, an maimaita labarun da ke cikin kumbon yanar gizo na Resia.

Ƙungiyoyi da sauran ma’abuta na ‘’Bretagne’’ na tsarin taimakon juna da ƙasar Nijar, suna himmar ƙara wa juna sani da hikimomi domin gudanar da wasu shirye-shirye.

Tsarin haɗin gwiwar ‘’Bretagne’’ da Nijar

Gurin wannan tsarin shi ne, ma’abuta na ɓangarorin biyu, masamman ma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na taimako, su haɗa gwiwa don ƙarfafawa da inganta ayyuka da nazarin da suke yi.
Wannan tsarin haɗin gwiwar yana kafa wani kwamitin zartar da ayyuka na tsawon shekara guda wanda yake zaman taronshi sau ɗaya cikin shekara, a cikin wani dapartama, kuma a ƙarƙashin jagorancin wata ƙungiya (2006 : a côtes d’Armor/RESIA ; 2007 : a ‘’Ille et vilaine/CRIDEV/Tarbiyya Tatali ; 2008 : a Finistère/Niger Breizh da Tilalt Niger tare da taimakon ƙungiyoyin da aka zana can baya.
Idan haɗin gwiwar yana da niyyar ɗorewar ayyukan, to sai ya ɗauki wani mataki domin hakan.
Muna neman goyon bayan ƙananan hukumomi da na haɗin gwiwar ƙungiyoyin da suke tallafa wa (RESIA, CRIDEV, CASI, ABCIS).

Matakan aikinsa

Matakan aikin haɗin gwiwar, uku (3) ne :

 • Haɗin gwiwar yana dogara da cikakkar niyyar mambobinshi
  Niyyar kafa wannan tsarin haɗin gwiwar, ta zo daga ƙungiyoyi da haɗin gwigwar ƙungiyoyi, kuma wasu ƙananar hukumomi suka goya baya ; su ne : Hukumar shawarar jahar ‘’Bretagne’’, da babbar hukumar shawarar ‘’Côtes d’Armor, da birnin Langueux wanda ya kawo ƙoƙari sosai ga taron 2006.
 • Haɗin gwiwar yana da nufin duba irin ayyukan ci-gaban jama’a da ƙungiyoyinshi na ‘’Bretagne’’ suka yi.
 • San nan yana son kafa tsarin gayya inda kowa yake sanya hannunshi ga duk abun da ya shafi ɓangarorin biyu, a Nijar ko a ‘’Bretagne’’

Yadda ƙungiyoyin haɗin gwiwar suka kasance.

Waɗanda suka halarci tarurrukan biyu, na Langueux da na Janzé, sun kasance cikin ƙungiyoyi ko ma’aikatu iri huɗu (4) :

 • Wasu suna cikin ƙungiyoyin Nijar ko na haɗin kan Faransa da Nijar masu cibiyarsu a ‘’Bretagne’’ ;
 • Wasu a cikin ƙungiyoyin ‘’Bretagne’’ masu gudanar da ayyukan a Nijar;
 • Wasu a cikin ƙananan hukumomi masu aiki a fannin hulɗar jaha da jaha ;
 • Wasu kuma ƙungiyoyi ne masu zaman kansu na ƙasa masu reshe a ‘’Bretagne’’;
 • Wasu ma’aikatun kiwon lafiya ne masu hulɗar bada horo tare da abokan aikinsu na ƙasar Nijar ;
 • Wasu ko makarantun boko ne na ‘’Bretagne’’ masu ƙulla tagwaici (ko tawaici) da wasu makarantun boko na Nijar.

Tun da aka yi wannan haɗuwar biyu, wasu ƙunguyoyin raya al’adu da na wasannin motsa jiki a game da ƙasar Nijar, sun shiga wannan haɗin gwiwar.

A shekara ta 2008 an yi wata haɗuwa a ‘’Morlaix’’

Manyan hanyoyi da matakan yin nazari da na ayyuka

Akwai buƙatar ƙara wa juna sani da hikimomi, da yin nazari bisa matsalolin da aka fuskanta, tare da taimakon ƙwararrun ma’abuta na ƙasar Nijar da aka gayyata, da waɗanda suke zamne a ƙasar.

Bunƙasa tsarin musaya da yaɗa labaru ta hanyar na’urar yanar gizo, saboda ingancinshi. A kan misalin abun da aka fara bara bayan haɗuwar da aka yi a Langueux, ana iya buɗe shafi bisa ƙungiyoyin taimakon juna tsakanin ‘’Bretagne’’ da Nijar, inda ake iya musayar sani.

Yawaita ma’abuta don ƙarfafa hulɗa, saboda kar a wayi gari hulɗoɗin jaha da jaha da ake kafawa su manta da haɗin kan ƙungiyoyi, kenan ya kamata ƙungiyoyi da sauran ma’abuta tsarin ƙasa da ƙasa na taimakon juna da Nijar, su riƙa hankali don ganin ba a manta da kowa ba.

Jerin sunayen ƙungiyoyin cuɗayyar juna ‘’Bretagne’’ da Nijar

Ƙungiyoyin cuɗayyar juna ‘’Bretagne’’ da Nijar, su 26 ne aka jera sunayensu kuma aka daidaita jerin sunayen cikin nobamba 2007, a albarkacin bukin cuɗayyar al’adu ‘’Breizh Nijar’’, kuma an sanya shi cikin kumbon yanar gizo na Resia. Idan ƙungiyarku tana buƙatar ganin sunanta cikin wannan jerin sunayen, sai ku tuntuɓi RESIA a wanga adireshin : resia@ritimo.org.

Photo d’Alain Roux