Gonar aikin lambu ta Marake Rogo

Wannan shi ne ɗaya daga cikin shafuka 11 da aka gano a binciken da MAE ta gudanar.

An kirkiro shi a shekara ta 2008, wannan aikin gona ( mai fadin ha 8) ya samo asali daga al’ummomin bayan daukar bashi . A halin yanzu fadin yankin da ake nomawa ha 5 ne, yawan manoma kuma ya kai su 80. Daga cikinsu kashi 2 bisa 3 duk mata ne. Ana gudanar da rukuni a cikin ƙungiyar mai sunan « Tashi Da Kanka ». Ana samun filayan nan ta hanyar yarjejeniyar taro na wannan tsari. Suna yin salati (sau 2), kabeji (sau 2), dankalin turawa, tumatir, da tattasai. Sukan cinye hillahirin anfanin gonakin. Kwuari na cinye anfanin gonakin wata rana. A cikin kwarin masu kai hare-hare akwai fara, da sauransu. Masu gonaki na amfani da toka wajen yakin su. Rijiyoyin ruwa guda hudu ne masu zurfin misalin mita 10 kuma wanda shayarwa ba ta da tasiri. Ana ban ruwa da guga da abin ban ruwa mai suna « arrosoir ». Ana kewaye filin da shinge na waya.

Wannan aikin

Ana gudamar da aikin a karkashin shirin “Ci gaba zuwa ga manufofin a garuruwan Dankatsari”, ya yi la’akari da :

  • Tsarin samun takardun filin wajen COFOB (Hukuma mai kula da takardun gonaki) ta yankunan karkara.
  • Tsarin ruwa, wanda ya shafi magudanun ruwa, ƙirƙirar wuri domin samun adanar ruwa da kuma rarraba ruwa don samun wata sabuwar rijiya a nan.
  • Horar masu aikin lambu don ƙarfafa halayen tsari, da haɗin kai, don samun fasaha,
  •  Taimako don samun iri da taki
  •  Kulawa da lambunan.

A wani bangare na shirin "Ci gaba mai dorewa a Dankatsari", an tanadar da wurin da injin famfo mai amfani da hasken rana a karshen shekarar 2019, kuma an gudanar da horo har sau uku. An gudanar da horon farko ne dage ranar 21 ga watan Janairu zuwa 23, na shekarar 2020. An sarrafa shi bisa ayiyar kayayyakin gonakin lambu. Horo na biyu an yi shi ne game da rayuwar ƙungiya, an gudanar da shi a ranakun 25 zuwa 26 na watan Janairu, shekarar 2020. Horo na uku bisa yadda ake kasuwanci da talla, ya ɗauki kwana uku, kuma an gudanar da shi daga ranar 30 ga watan Nuwamba, zuwa 2 ga watan Disamba, shekarar 2020. Kowane horon ya tara mahalarta mutane 60, mata 40 da maza 20. Mai horarwar shi ne manajan aikin gona na Dankatsari tare da wakilin RAEDD.