Tsari mai kyau don yin yakin karancin abinci shi ne a bunkasa noman rani : noma lambu ko na ƴan itace a kowane lokaci cikin shekara, ba sai lokacin da aka saba yin noma ba wato damana mai tsawon wata hudu.

Don a kara sake ra’ayin mutane, malamen da ƴan makaranta ake kama wa don su yi noman rani a hilin makarantu. Matsalar ruwa na tare da wannan bunƙasa, a samu ƴan ruwa, don lambuna cikin rani.

Hulɗar Cesson- Dankatsari da ‘yan makarantar Beausoleil na Cesson-Sevigne suna taimakon lambun ‘yan makaranta tun shekarar 2009.

Tun shekarar 2013, lambun makarantar yana cikin babban garin Dogontapki.
 An hada shi da wani gandun zogala.

Tsiron lambu (kabeji, gauta, tumatir…) ake dasawa, ‘yan makarantar ke kawo taki. Lambun da aka girba, ‘yan makarantar ke anfani da su ko kuma a saida su a kasuwa domin sayen littatafai da sauransu.

Za a girka lambun ƴan makaranta na biyu nan zuwa karshen shekarar 2014, cikin wani gari na kwamin ɗin Matankari game da taimakon gidauniyar Total.
 Shi ma an hada shi da gandun zogala.

Tun shekarar 2020, manufar ita ce a samar da lambunan makarantu a kowace shekara a wani kauye daban da na Dankatsari tare da tabbatar da dorewarsu ta hanyar sa ido akai-akai. An kafa lambunan makaranta a Kamrey da Kolmey, ana neman shirya sabon lambun a Nakigaza. 

Enfants