Domin bambamtardawa da kayadewar ko wane mutun da daular sa da kuma karfafa saninsa da yancinsa ko abin da ya zamo masa tilas. Bayan wannan, barikin kula da takardun aihuwa abu ne wanda ya zamanto mihimman kan bunkasawar da ci gaban ƙasa.

Dacewa ne ga gundumar Dankatsari na fanin ma’aikantan barikin kula da takardun aihuwa domin tafiyar da aikin kai da kai domin ayyuka kamar wadannan :

  • koyar da ma’aikatan bisa kundin bayanu da ke tafiyar da ayyukan barakin takardun aihuwa a Nijar;
  • a tabbata musu sanin ka’idodi da kotamce bisa bayar da takardun iyali na ƙasa
  • jawo hankulansu bisa duk abin da ya shafi barikin takardun aihuwa a Nijer

Wannan aikin ya soma ne tun 2009 cikin karamar gundumar Dankatsari kambacin hul’da gani a ƙasa tsakanin Cesson-Dankatsari.

Ma’aikatu goma sha biyar ne suke samun kayan aiki da horo a ko wacce shekara saboda samun girgam na musamman domin takardun aihuwa.

A shekarar 2014, ‘yan ma’aikatar takardun haifuwa sun samu registar na rubutun takardun haifuwa. Mutane 15 ne suka samu wannan horon. Yanzu an fi samun rubutun takardun haifuwa da da, amma akwai sauran aiki. Arme dai, da mutuwa har yau ba’a rubutansu cikin register. Ƙaramar Hukumar Dankatsari ta gina da kuɗinta, ofis game da sayen kayan aiki na hukumar.