A Nijar, ana bada wannan horon na yaƙi-da-jahilci ga matan da ba su taɓa shiga makarantun boko ba, kuma da harshen gida ne ake yin shi.

Matan garin Lugu

A shekara ta 2007, a garin Lugu an yi wani rukunin ƴan yaƙi da jahilci a cikin harshen Hausa.

Matan makarantar ‘’Espoir’’ a Yamai

Rukunnai 2 ke akwai na yaƙi da jahilci ; ɗaya cikin harshen zabarmanci, ɗaya kuwa a cikin harshen hausa.

Matan garin Dan Katsari

Bawada Gida, gari ne na kwamin ta Ɗankatsari. Da yawa daga cikin matan garin suna fatan sun samu horon yaƙi da jahilci cikin harshen hausa.

Wani rukuni na mata 25 ya samu irin wannan horon a shekara ta 2009 zuwa 2010 ta hulɗar garin Cesson da na Dan Katsari.

Rukuni na biyu da ya ƙumshi mata 33 ya samu horo a shekara 2010 zuwa 2011 a kambacin rabbabar hulɗa tsakanin Cesson da Dan Katsari a garin Dogontapki.
A shekara alip dubu biyu da goma sha ɗaya zuwa alip dubu biyu da goma sha biyu (2011-2012 mace 50 ne aka ba horon yaki da jahilci a garin Dogontapki.

A shekarar 2012-2014 an yi horon wani rukuni na mata 33 a Guizara.
Abin ya ba da shawa, shi ya sa aka yi wa kungiyoyi biyu na mata 25 horon yaki da jahilci da Hausa a garin Karki Mallam a shekarar 2014-2016, a Kamrey shekara 2015-2017, a Chanono 2016-2018, a Tunzurawa 2017-2019.

A cikin shekarar 2018 zuwa 2019, cibiyoyin koyon karatu guda biyu suke aiki a Tunzurawa da Tudun-Makera, da wani kuma a Gofawa, a zaman wani ɓangare na shigarwa na dandalin multifunctionalal.

Horon yaki da jahilcin mata na karfafa masu samun inganci da mulkin kai na yau da kullum, sukan yi aikin mai ba su dan albashi. Rukunin matan da aka yi wa horon yaki da jahilci a garin Karki Mallam na neman samun tsarin dayawa na ƙanana basussuka bayan shekarunsu biyu na horo.

Dangane da amfani da makamashi a yankunan karkara

Tun daga shekara ta 2011, RAEDD ke gudanar da cibiyoyin karatun jaki da jahilci 50 a cikin ƙauyukan da ke da kayan aiki da yawa (PTFM).

Goubeye, 2010 (Abdoul Aziz Soumaïla)
Goubeye, 2010 (Abdoul Aziz Soumaïla)