Hulɗa gani a ƙasa tsakanin Cesson da Dankassari daga shekara ta 2009.

Gundumar Dankassari tana makoptaka da ta Dogonduci. Ta ƙumshi garuruwa masu dama ; kuma tana makoptaka da garin Lugu da na Lillato inda yawancin al’uma ya tashi kimanin mutun 70 000.
Bayan fa’intar da juna a shekara 2008, aka sa hannu a kan yarjajeniya ta hul’da ganin a ƙasa tsakanin magajin garin Dankassari da na garin Cesson-Sévigné daga shekara 2009 zuwa 2011.

Yankunan da yarjajeniyar ta shafa su ne

  • tarbiyya, da horon ƴan mata da mata a kan kiyayewa da lafiyar uwa da ɗa
  • shirya dubarun samun ruwa, shipka ittatuwa da akan anfani da ‘diyansu, da lambuna
  • tallahi zuwa ga ma’aikatunan magajin gari don kulawa da abin da ya shafi takardinan haihuwa da kinginsu
  • abin da ya ƙumshi galgajiya.

Kungiyar RAEDD ce aka ba kular da wannan, ita kuma AESCD zata kula da ci gaban ayyuyukan.

Ayyukan shekarar 2009 zuwa 2010

Hul’dar gani a ƙasa tsakanin Dankassari da Cesson-Sévigné ta ƙumshi yanki kamar haka

Samun ruwa
. hihita samun ruwan sha a garin Dankassari

Lambuna da dashen ittatuwa

  • hihita lambun ƴan makaranta cikin fadama
  • lambun iri

Tarbiyya da horon mata

  • kafa injin 2 na nikar hatsi a garin Lugu da Bawada gida
  • horon gungun mallaman makaranta 14 don kula kai da kai ‘dan rayuwar iyali bisa tarbiyya da ta shafi kansa da kansa ; da kula da ‘bunkasar yawan al’uma ; da sayen littafi 400.
  • horon ungozoma 10 da sayen musu kayan aiki
  • horon yaki da jahilci ga gungun mace 25 a garin Gubey

Takardun ƙasa

  • horon ma’aikata 15 don takardun masaman na ƴan kasa
  • taimako rejista a gari 15 da wasu kayan aiki
  • shirya wata ganuwa domin rubuta sunayen yara bisa rejista

Akan samun ruwa kingin kudi sun samu daga ƙungiyar Afik Insa da ƙungiyar ruwa ta Loire-Bretagne.

A shekara 2009, Komitin masaman na 35 ya ɗauki nauyin rajajeniya don sayen Spirilin domin ɗakunan lahiya na gundumar Dankassari

Aiyyukan shekarar 2010 zuwa 2011

Rabbabar hulda tsakanin Cesson da Dankasari ta ƙumshi

Samun ruwa

  • Samun tsabtatu ruwa a garin Dogontapki

Lambu da dashe

  • Dashen ittatuwa

Ba da illimi da horo wurin mata

  • Kahwa injinan nikan hatsi 2 a garuruwan Dogontapki da Kamrey
  • A kambacin raya yanayi da zaman kansa da kansa, an ba da horo zuwa ga malaman makaranta 14.
  • An talahwa ma ungozamai da kurar shanu 3 don taimakon gaugawa ga masu matsalar haihuwa a garin Duzu, Kamrey da Marakin rogo
  • A kambacin yaƙi da jahilci an ba mata 33 horo

Shiwilci

  • An ba ma’aikata 15 horo
  • An raba ma gari 15 regista da kayan aiki
  • Komiti mai yawatawa a karkara ya shirya zaman yi ma yaran kauye takardun haifuwa da na ƙasa

Komitin ma saman ya ba da a shekarar 2010 talahi ga projen tabatacin irin shipka da rumbun timi.

Kambacin tsabtacin ruwa, an samu talahi daga masu hannu da shuni.

Ayyukan shekarar 2011 zuwa 2012

Hul’dar Cesson da Dankatsari ta sahi abubuwa kamar :

Samun ruwa

  • Nazarin bu’katun ilahirin garuruwan Dankatsari

Aikin Lambu da dashen itatauwa

  • Kulawa da garken lambu na yan makaranta da taimakon lakole ta firimare ga samun littatafan aiki.
  • Gona

Ilimi da horo musamman na mata

  • Girka injin nikan hatsi a Jarkassa, horon masu injin
  • Horon malamin lakole 14 ga hakin ‘dan adam da na iyali, kamar abin da ya shafi horon a kan jinsi, ya’kin yawan mutane, sayen littatafai 400.
  • Amalanken 3 da aka baiwa ungozoman da ke garuruka masu nisa, saboda kan masu haifuwar da ta zo ta gardama a Tchito, Kandandamé et Kaura Lahma.
  • Horon ya’ki da jahilci na gungu 2 na mata 25 a Dogontapki

Takardar haifuwa

  • Horon ma’aikatan magajin gari 15 don kulawa da abin da ya shafi takardun haihuwa
  • Kayan aiki ga garuruwa 15 bisa abun da ya shafi kayan register
  • Tsarin wani taro don a yi regista na yaran da basu da takardun haihuwa.

Babar hukuma ta 35 ta taimaki a shekarar 2011 wani projet ko shiri don inganta yan iri wajen yin gonakin lakole a Dogontapki.

Ayyukan shekarar 2012 zuwa 2013

Hul’dar Cesson da Dankatsari ta sahi abubuwa kamar :

Samun ruwa

  • Bayan nazarin bu’katun ilahirin garuruwan Dankatsari, an kafa wurin samun ruwa a Lugu da kuma an yi gyaran pompo 3 a garuruwan Karki Mallam, Dan Keda da Marake Tudu.

Aikin Lambu da dashen itatauwa

  • Kulawa da garken lambu na yan makaranta
  • Gona

Ilimi da horo musamman na mata

  • Girka injin nikan hatsi a Karkin Mallam, gyaran injin nika na Lugu
  • Horon malamin lakole 14 ga hakin ‘dan adam da na iyali, kamar abin da ya shafi horon a kan jinsi, ya’kin yawan mutane, sayen littatafai 400.
  • Amalanken 6 da aka baiwa ungozoman da ke garuruka masu nisa, saboda kan masu haifuwar da ta zo ta gardama a Kumey, Chanono, Saurin kahi, Bagnan Dutsi, Gulbi et Elgueza, A cikin su uku aka saya da ku’din biyan bashi na amalanken farko
  • Horon ya’ki da jahilci na gungun mata 33 a Guizara

Taimako ga ma’aikatan magajin garin Dankatsari

  • Kayan aikin shugaban ma’aikantar takardun haihuwa : Sayen computer da horon mallamin ga yadda ake aiki da wannan computer.
  • Kayan aikin ma’aikacin da ke kullawa da makarantun : sayen babur
  • Sayen kayan makaranta, da tebur na koleji

Wajen samun ruwa, an samu taimakon ku’di na abokan hul’da dayawa.

Enfants de Dankassari
{{}}