An kammala wannan mataki.

Kwaminonin Dankatsari da Cesson-Sevigne sun halarci da kuzari ga wannan taron na biyu na hulda tsakanin Faransa da Niyar, da aka yi a Yamai daga ran 14 zuwa 16 ga watan october 2014.

  • Magajin kwamin ‘din Dankatsari, Assiu Abarchi ya wakilci Kwamin ‘din.
    - Garin Cesson-Sevigne kuma Marie-Françoise Roy shugabar AESCD da Michel Coste ne suka wakilci garin.

Mahamadu Saidu kuma mai tafiyar da ayyukan RAEDD da Mamane Chadau mai kula da hulda suka wakilci RAEDD

Magajin Cesson-Sevigne ko ya aiko da sadarwa.

Magajin garin Dankatsari ya sa baki lokacin taro na samu ruwa da yin tsabta tare da kawo sadawar kamar haka.

Bayan ayyuka an yi taro ran juma’a 17 ga watan october tsakanin wakiltan Cesson, Magajin garin Dankatsari da shugabanin ofisoshi masu taimaka ma karamar hukuma, kuma da mutane da dama wakiltan RAEDD. An tauttauna bisa ayyukan ci gaba na Dankatsari 2013-2016 tare da amincewar majalisar baki daya.