Samun kayan don amfanin kowa (makarantu, kayan kiwon lafiya) da bandaki shi ne ɗaya daga cikin abubuwan fifikon da Ma’aikatar ruwa da tsaftar muhalli ta Dogon Dutsi da jama’ar karkara da abin ya shafa.

Kasancewar bandakin ɗalibai mata a cikin makarantu da kwalejoji yana inganta amincin tarban su kuma yana haɓaka neman iliminsu.

Wannan aikin bai takaita a kan gini kawai ba amma yana tare da wayar da kan jama’a game da tsafta da horo kan yadda ake amfani da bandaki, wurin malamai, da kwamitocin gudanarwa da kuma dalibai.

A cikin kwalejojin Dankatsari

Tsarin dai don a gina wa ’yan mata/maza salangogi a cikin kwaleji uku na yankunan karkarar Dankastari, kamar a Nakigaza, Karki Malam Kadandame, Gubey, Bawada Daji, Ruda Gumandey, Gofawa,

Tsarin kuma yana da nauyin karfafa ’yan mata (39% na mata cikin kwalejin da abun ya shafa) don su ci gaba da karatu har zuwa BEPC, ba da yin auren mahalli ba da wuri.
Kwaleji hudu aikin nan ya shafa kuma gwamnatin Nijar za ta dauki nauyin kudaden, uku kuma tare da kudade garin Rennes, a cikin tsarin na “samun ci gaba da manufofin raya kasa a kauyuka na Dankatsari”.

A cikin bukkokin kiwon lafiya da makarantun Dankatsari

An ba da tallafi daga Rennes Métropole zuwa AESCD a ƙarshen 2018. An gina bukkoki uku na kiwon lafiya a cikin 2019 tare da gida biyu da wurin wanka a ƙauyukan Duzu, Sauri-Kaifi da Bare-Bari. Bugu da kari, jihar ta Nijar ta girka bangarori uku na bandakuna a makarantun Sabara da Rumbukawa (reshen garin Sucucutane) albarkacin tallafin daga SwitzerlandAid.
Tallafi daga Rennes Métropole ga AESCD ya ba da damar a cikin 2020 gina bayan gida da kuma wurin wanka a kauyuka : Gofawa, Kolmey da Dogontapki.
Don aikin da Jihar Nijar ke daukar nauyinsa a layi daya, shi ne na ginin sallangogi da ke da famfunan a makarantun manyan kauyuka uku na Kadandame, Rumuki Kadandame da Dangari, a lokacin da aka kafa wani hadaden wurin na kauyuka AEP. Ginin bayan gida ya kammala a ƙarshen Janairu 2021.

A cikin 2021, wani sabon tallafi daga Rennes Métropole zuwa AESCD ya ba da damar gina salangogi da wurin wanka a gidagen kiwon lafiya na ƙauyuka : Kaura Lahama, Marake Rogo da Goho.  

A kolejin Bagaji

An samu kuɗaɗe daga Rennes Métropole zuwa AECIN a karshen shekara ta 2018. Wannan ya sa aka kara gina salangogi a Kwalejin Bagaji, yanzu akwai sahen salangogin ’yan mata da kuma sashen ‘yan maza.

Sabbin kwalejoji guda uku waɗanda aka tanadar a 2021

A yanzu haka, ana gina wuri uku na bayan gida (daya na malamai, daya na dalibai mata daya kuma na dalibai maza) a kwalejojin Dubalma da ke Sucucutane, Salga, Matankari da Issakitchi a Dogonkiria. An sami kuɗi daga AELB, FORIM, Rennes Métropole da CEBR.