Karuwar yawan jama’a daga kasa da miliyan 5 a shekarar 1970 zuwa sama da miliyan 17 a shekarar 2012 ya fi na ci gaban tattalin arzikin kasa, kuma tattalin arziki na ‘yan kasa ya fadi zuwa kashi 40 bisa dari tsakanin 1970 da 2012. Ƙaruwar haihuwar nan na hana kasancewa a cikin kasar .

Inganta tsarin iyali

Ma’aikatar Lafiya ta soma wani shirin (2012-2020) domin taimakawa wajen samun saukin yawan mutane na inganta tsarin iyali. Manufar shine a matsa daga kashi 11 bisa ɗari na zamani maganin hana haifuwa zuwa kashi 50 bisa ɗari dangane da dabarun uku na tsarin iyali.

  • karfafa samar da kiwon lafiya cikin likitoci
  • karfafa bukatar ta hanyar ilimi da kuma wayar da kan jama’a
  • gabatarwa na wani yanayi mai dama.

Samun tsara wannan dai na bukatar janyo ra’ayoyin jama’a na musammun.

Gudunmuwar Tarbiyya Tatali

An dauki wata kwarara a watan Nuwamba 2015 a kan kudi na AESCD. Aikinta dai shi ne karfafa maganin hana haifuwa ta hanyar ilimi da kuma wayar da kan jama’a. Dakunan kiwon lafiya su kuwa ( CSI da dakunan kiwon lafiya ) an gayyatosu don ci ma wannan shirin.

An fara da daukar lambar kungiyoyin Asusun kawo canjin matsayi, waɗanda suke aiki sosai a Dankatsari duk da rishin samun kuɗaɗe kungiyar Stromme.

Ta ziyarci dukan ƙauyukan a yankunan karkara Dankatsari domin yin taro na wayar da kai. Manufarta ita ce ganewa, horar da, da kuma samun mutanen da za a iya aiki da su a cikin kauyuka.

Gurinta na farko shi ne haƙiƙa yakin auren ‘yan mata kanana (kafin shekara 18) da kuma samun cikin farko kafin shekara 19. Manufarta ta biyu ita ce inganta lafiyar mata da yara tare da haihuwa jehi jehi da kuma yin amfani da maganin hana haifuwa na zamani. Manufarta ta uku ita ce ta wayar da kan da canjin halin, musamman ma na maza. Manufarta ta hudu ita ce ta wayar da kan jama’a don yin la’akari tsakanin tattalin arziki da na yawan mutane a Nijar.

An dauki ma’aikaciya don gudanar da aiyuka a ƙauyukan Dogondutsi, AECIN da ƙungiyar musaya tsakanin Orsay da Dogon Dutsi ke daukar nauyin albasinta.

An yi horo biyu na mata 25 masu kulawa da wannan irin aiki a ƙauyuka. an shirya su ne a cikin tsarin “Ci gaban manufofin garuruwan Dankatsari", ”. An yi horon a karshen shekarar 2017, da farkon shekarar 2018.
An yi horo biyu na mata 30 masu kulawa da aikin tsarin iyali a Kauyukan Dogon Dutsi a watan Nuwamba na shekarar 2019.

Karfafa horar da mata 30 masu ba da gudummawa a cikin tsarin iyali a cikin kwanaki uku aka shirya, da nufin ba da amsa kan abin da suka aikata a ƙauyuka bayan horon da suka yi na farko a ƙarshen 2017 da farkon 2018 da kuma tabbatar da cewa sun yi amfani da ilimin horon baya da aka yi masu. An soke horon ne saboda gwamnatin Nijar ta hana taro sakamakon cutar COVID. A ƙarshe an yi shi daga ranar 5 zuwa 7 ga Maris, 2021, tare da halartar malamai biyu na tsara iyali.

An basu kyautar kayan tsarin iyali, tare da kayan nuni ko pagivoltes 27.

Sakamakon farko

An samu kokari da aka yi don canza ra’ayi game da haifuwa a cikin kididdiga. A cewar Cibiyar Demokradiyya da Lafiya ta Nijar 2017, yawan haihuwa ta rage daga yara 7.6 a 2012 zuwa 6.0 ga kowace mace a shekara ta 2017. An fi samun ragewar haifuwa a yankin Dosso - wanda ta ƙumshi Dankassari da Dogon Dutsi cewa daga yara 7.5 an faɗo ga samun yara 5.7 ga kowace mace.

Daga 2018 zuwa 2020, mai gudanar da aikin tsarin iyali Maimuna Kadi ta haɗu da mutane sama da 11,000, kusan 35% daga cikinsu maza ne na gundumar Dankatsari, a ƙauyuka da yawa. Haka kuma tana daga cikin masu yawon bude ido da wayar da kan Al’umma bisa samun takardun haifuwa a farkon watan Janairun 2021, wanan ya ba ta damar isa wuraren da ke da wahalar zuwa inda ba za ta iya zuwa a babur ba kamar su Karki Malam.

A yayin da take tattaunawa da babbar ma’aikaciyar jinya ta hadaddiyar cibiyar lafiya (CSI) da ke garin Dogon Dutsi, mai gabatarwar, Rekia Tumane ta ziyarci kauyuka da dama a cikin shekarar ta 2018 kuma ta ga sama da mutane 2,300 a cikin watanni takwas, kimanin kusan mutane 300 a kowane wata, wanda kusan kashi 40% maza ne. A cikin 2019, ta ziyarci wasu ƙauyuka kamar 25 na Dogon Dutsi, watau matsakaita na ƙauyuka 5 a kowane wata a kan yadda za a yi taro sau 3 a kowane ƙauye (kamar taro 15 a wata), tare da jigogi ɗaya ko biyu wadanda a kan su ake tattanawa a kowane lokaci.
A cikin 2020, Rekia Tumane ta ci gaba da ziyararta kuma ta haɗu da mutane 3,540 waɗanda suka haɗa da mata 2,260 da maza 1,280.

Maimouna Kadi